An kulle Masallacin Qudus saboda annobar Coronavirus

An kulle Masallacin Qudus saboda annobar Coronavirus

Jagorancin Masallaci na uku mafi falala ga mabiya addinin Islama sun alanta kulle Masallacin Qudus dake kasar Falasdin sakamakon annobar Coronavirus da ta addabi duniya.

Amma sun baiwa mutane damar Sallah a harabar Masallaci.

Kwamitin Waqafin Masallacin sun bayyana cewa an yanke wannan shawaran kulle cikin Masallacin har ila ma shaa Allahu domin takaita yaduwar cutar ta Coronavirus.

Diraktan Masallacin, Omar Kiswani, ya bayyanawa Rueters cewa “za a cigaba da gudanar da Sallan jam-i amma harabar Masallaci. “

An kulle Masallacin Qudus saboda annobar Coronavirus

An kulle Masallacin Qudus saboda annobar Coronavirus
Source: Facebook

A baya mun kawo muku rahoton cewa Shugabancin Masallacin Harami karkashin jagorancin babban limami, Sheikh Abdur-Rahman As-Sudais ta kaddamar da feshi da tsaftace Mataaf na musamman domin kawar da yaduwar cutar Corona.

Mabiya addinin Islama a fadin duniya sun yi mamakin hakan inda da dama suka ce wannan shine karo na farko da zasu ga Masallacin Harami babu kowa.

Mun kawo muku rahoton cewa Gwamnatin kasar Saudiyya ta dakatad da aikin Umrah da ziyarar Masallacin Annabi mai girma ga dukkan yan kasar da mazauna sakamakon bullar cutar Coronavirus a kasar.

Ma'aikatar kiwon lafiyar kasar ta dau matakin ne domin takaita yaduwar cutar a kasar mai alfarma.

Gwamnatin kasar Saudiyya ta alanta cewa a mayarwa dukkan wadanda suka biya kudin Umrah kudadensu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel