Hukumar yaki da rashawar jihar Kano za ta sake sammatar Sanusi Lamido

Hukumar yaki da rashawar jihar Kano za ta sake sammatar Sanusi Lamido

Hukumar sauraron korafi da yaki da rashawar jihar Kano za ta sake sammatar tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, na ba da dadewa ba domin kare kansa kan zargin almundahanar kudin filin Gandun Sarki na kimanin, N2.2 biliyan.

Ana zargin tsohon sarkin Kanon ne da laifin sayar da filaye a Darmanawa Phase I da II, da kuma Bubbugaji a Kano.

Thisday ta ruwaito cewa a karshen makon da ta gabata, hukumar ta samu isassun hujjojin da zasu isa a sammaci tsohon sarkin kuma a kaddamar da bincike a kansa.

Hakazalika, Antoni Janar kuma ministan shariar, Abubakar Malami SAN, ya yi watsi da rahoton cewa shine ummul habaisin cire Sarkin Sanusi.

Hukumar yaki da rashawar jihar Kano za ta sake sammatar Sanusi Lamido

Hukumar yaki da rashawar jihar Kano za ta sake sammatar Sanusi Lamido
Source: UGC

Zaku tuna cewa a ranar 5 ga Maris, hukumar yaki da rashawar ta jihar Kano ta daga ranar sammacin Sanusi daga 5 zuwa 9 ga Maris, amma wata babbar kotun tarayya dake Kanon karkashin jagorancin Alkali Lewis Allgoa, ta hana hukumar binciken tsohon sarkin.

Amma hukumar ta lashi takobin sake sammatar Sanusi saboda hukuncin daukaka kara ya bata daman binciken kowani irin mutumin da jihar ke zargi ga cin hanci da rashawa.

Majiya mai karfi ta bayyana cewa hujjojin da ke gaban hukumar yanzu za ta isa wajen damke tsohon sarkin da kuma gurfanar da shi a kotu.

“Har yanzu ana bincike, hukumar ta gayyaci wasu kamfanoni. Nan ba da dadewa ba za a sammaci tsohon sarkin domin kare kansa kan zargin sayar da dukiyar gwamnati. Kuma a sani cewa wannan sabon tuhuma ne.“

“Sauke sarkin ba zai hana hukumar gudanar da ayyukanta na bincike a kansa ba. ,”Yace

Za ku tuna cewa a 2019, hukumar ta baiwa gwamnatin jihar shawarar dakatad da sarkin kan laifin almubazzaranci da kudin masarautar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter:

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel