Tube rawanin Sanusi II: Majalisar jihar Kano ta dakatar da 'yan majalisa 5

Tube rawanin Sanusi II: Majalisar jihar Kano ta dakatar da 'yan majalisa 5

- Majalisar jihar Kano ta dakatar da 'yan majalisa biyar na watanni shida dangane da hargitsin da aka samu a zauren majalisar

- A dawowa zaman zauren da aka yi a yau Litinin, Abdulazeez Gafasa, kakakin majalisar ya ce, an dakatar da 'yan majalisar ne sakamakon take doka da suka yi

- Wadanda aka dakatar sune: Garba Yau Gwarmai, Labaran Abdul Madari, Isyaku Ali Danja, Mohammed Bello da Salisu Ahmed

Majalisar jihar Kano ta dakatar da 'yan majalisa biyar na watanni shida dangane da hargitsin da aka samu a zauren majalisar a ranar Litinin din makon jiya. Wannan hargitsin kuwa yayi sanadin kwace sandar majalisar.

A dawowa zaman zauren da aka yi a yau Litinin, Abdulazeez Gafasa, kakakin majalisar ya ce, an dakatar da 'yan majalisar ne sakamakon take dokar da suka yi, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Tube rawanin Sanusi II: Majalisar jihar Kano ta dakatar da 'yan majalisa 5

Tube rawanin Sanusi II: Majalisar jihar Kano ta dakatar da 'yan majalisa 5
Source: UGC

DUBA WANNAN: Tube rawanin Sanusi: AGF Malami ya yi zazzafan martani

'Yan majalisar da aka dakatar sun hada da: Garba Yau Gwarmai mai wakiltar mazabar Kunchi/Tsanyawa, Labaran Abdul Madari mai wakiltar mazabar Warawa, Isyaku Ali Danja mai wakiltar mazabar Gezawa, Mohammed Bello mai wakiltar mazabar Rimingado/Tofa da Salisu Ahmed Gwamgwazo mai wakiltar mazabar birnin Kano.

Kamar yadda kakakin majalisar ya sanar, "Yan majalisar biyar an dakatar dasu ne sakamakon karantsaye da suka yi ga dokokin majalisar ta hudu wacce ta haramta kawo tsaiko da hana zaman majalisar.

"Sun kawo rashin hankali da yunkurin kwace sandar majalisar don zagon kasa ga zaman majalisar na wannan lokacin," Gafasa yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel