Jerin kasashen Afrika 26 da cutar Coronavirus ta bulla kawo yanzu

Jerin kasashen Afrika 26 da cutar Coronavirus ta bulla kawo yanzu

Akalla kasashen nahiyar Afrika 26 cikin 54 da aka samu bullar annobar cutar Coronavirus kawo safiyar Litinin, 16 ga watan Maris, 2020.

Cutar wacce ke cigaba da yaduwa a fadin duniya ta tayar da hankulan kasashe, ta durkusar da tattalin arzikin duniya tare da karya farashin danyen man fetur a kasuwar duniya.

A fadin duniya yanzu, an tabbatar da mutane 142, 539 sun kamu da cutar kuma 5,393 sun mutu.

A cikin wannan adadin, mutane 80,851 yan kasar Sin ne inda cutar ta samo asali kuma mutane 3,199 sun mutu a can.

Cikin kwanaki biyu na karshen mako, akalla kasashen Afrika 12 sun samu bullar cutar

Ga jerin kasashen nahiyar Afrikan da aka samu bullar yanzu

Algeria, Misra, Tunisiya, Maroko, Senegal, Najerya, Afrika ta kudu, Kamaru, Burkina Faso, Togo, DR Congo, Cote D'Ivoire, Habasha, Kenya, Namibia, Seychelles, Central African Republic, Congo, Equatorial Guinea, Eswatini, Gabon, Guinea, Mauritania, Ruwanda, Ghana da Sudan

A Najeriya, har yanzu mutane biyu aka tabbatar sun kamu da cutar, bayan haka, an gwada mutane 48 a jihohi irinsu Edo, Enugu, FCT, Kano, Lagos, Ogun, Rivers, da Yobe, kuma ba same su da it aba.

Ministan kiwon lafiya, Enahire, ya bayyana cewa dan kasar italiyan da ya kawo cutar Najeriya ya samu lafiya kuma nan ba da dadewa ba za a sallameshi.

Algeria 48 South Africa 51 Senegal 24 Cameroon 3 Nigeria 2 Burkina Faso 7 Togo 1 DRC 3 Cote d'Ivoire 5 Ghana 2 Gabon 1 Kenya 3 Ethiopia 4 Guinea 1 Rwanda 5 Namibia 2 E Guinea 1 Seychelles 2 CAR 1 Congo 1 Mauritania 1 Eswatini 1 Liberia 1 Egypt 110 Morocco 28 Tunisia 18 Sudan 1

Asali: Legit.ng

Online view pixel