Sojoji 6 sun mutu a harin kwantan bauna da Boko Haram ta kai a Borno

Sojoji 6 sun mutu a harin kwantan bauna da Boko Haram ta kai a Borno

Akalla dakarun rundunar Sojojin Najeriya guda 6 ne suka gamu da ajalinsu a sakamakon wani mummunan harin kwantan bauna da mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suma kaddamar a ranar Lahadi a jahar Borno.

Kamfanin dillancin labaru na AFP ta ruwaito mayakan ta’addancin sun kai ma Sojojin harin ne yayin da suka bude ma ayarin motocin Sojojin wuta a kusa da kauyen Mayanti dake kusa da iyakar Najeriya da kasar Kamaru, yankin da yan ta’adda suka mamaye.

KU KARANTA: Mutane 15 sun mutu, gine gine 50 sun rushe a fashewar bututun mai a Legas

“Mun yi asarar Sojoji guda 6 a wannan harin kwantan bauna da Boko Haram ta kai mana.” Kamar yadda wani jami’in rundunar Soja ya tabbatar ma majiyar Legit.ng.

Wata majiya ta daban ta bayyana cewa ayarin motocin Sojoji suna kan hanyarsu na zuwa wani gari ne mai suna Banki a lokacin yan ta’addan suka bude musu wuta tare da jefa musu nakiyoyi.

A wani labarin kuma, duk da kiraye kirayen da kungiyar ta’addanci ta duniya, ISIS, take yi ma mayakanta game da kai haddamar da hare hare a kasashen Turai, amma a yanzu ta ja da baya, inda ta nemi su kauce ma shiga nahiyar Turai saboda annobar cutar Corona.

Jaridar NewYork Times ISIS ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar a jaridarta na ‘Al-Naba’ indsa ta shawarci duk mayakanta dake turai, kuma har sun kamu da cutar, toh su yi zamansu a can domin cigaba da yada ta ga kafirai.

“Wannan bala’i wani nau’i ne na azaba da Allah Yake saukar ma duk wanda ya so, don haka wanda bai kamu ba kada ya sake ya shiga yankin da annobar ta watsu, wanda kuma ya kamu kadsa ya fita daga yankin.” Inji ISIS.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel