Mutane 15 sun mutu, gine gine 50 sun rushe a fashewar bututun mai a Legas

Mutane 15 sun mutu, gine gine 50 sun rushe a fashewar bututun mai a Legas

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, NEMA, ta bayyana cewa jami’anta sun kwashe gawarwakin mutane 15, daga ciki har da na wasu mutane 4 yan gida daya bayan fashewar bututun mai da tukunyar iskar gas a unguwar Abule Ado ta jahar Legas.

Daily Trust ta ruwaito mazauna unguwar sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon tarin tukunyoyin iskar gas na kamfani dake jibge a yankin, wadanda suka fashe, har suka shafi bututun mai mallakin wani kamfani mai zaman kansa.

KU KARANTA: Ayarin motocin mataimakin shugaba Osinbajo sun gamu da mummunan hatsari a Abuja

Mutane 15 sun mutu, gine gine 50 sun rushe a fashewar bututun mai a Legas

Mutane 15 sun mutu, gine gine 50 sun rushe a fashewar bututun mai a Legas
Source: UGC

Bugu da kari akwai akalla daliban kwalejin sakandarin mata na Bethlehem guda 50 ne suka samu munana rauni a sakamakon harin, amma an garzaya dasu asibitin rundunar Sojin ruwa dake Ojo Cantonement.

Mukaddashin shugaban NEMA reshen jahar Legas, Ibrahim Farinloye ya bayyana cewa mutane hudu yan gida daya da suka mutu su ne wasu ma’aurata da yaransu biyu, wanda suka kama da wuta yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Coci a ranar Lahadi da misalin karfe 9 na safe.

“Wutar ta kai har zuwa wani bututun mai na NNPC da ya ratsa ta unguwar, amma dai an kashe bututun man don hana cigaba da wucewar man, har sai kusan karfe 3:30 na yamma aka kashe wutar tare da hadin gwiwar hukumar kashe gobara ta jahar Legas, hukumar kashe gobara ta kasa da sashin hukumar kashe gobara na rundunar Sojan ruwa.” Inji shi.

Shugaban hukumar kula da muhalli na jahar Legas, LASEMA, Dakta Olufemi Oke-Osayintolu ya bayyana cewa za su gudanar da cikakken bincike game da lamarin domin sanin gaskiyar musabbain aukuwar hatsarin.

“Muna kira ga jama’a cewa kada su firgita, mun shawo kan lamarin kuma mun kashe gobarar da hadin gwiwar hukumomi daban daban, har yanzu dai bamu ji warin iskar gas ko man fetir ba, don haka ba zamu iya cewa ga abin da ya janyo gobarar ba.” Inji shi.

Daga karshe yace har yanzu suna cigaba da sauraron rahoton binciken da jami’ansu suke gudanarwa a kan lamarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel