Kungiyar ISIS ta hana mayakanta kai hare hare a kasashen turai saboda tsoron Corona

Kungiyar ISIS ta hana mayakanta kai hare hare a kasashen turai saboda tsoron Corona

Duk da kiraye kirayen da kungiyar ta’addanci ta duniya, ISIS, take yi ma mayakanta game da kai haddamar da hare hare a kasashen Turai, amma a yanzu ta ja da baya, inda ta nemi su kauce ma shiga nahiyar Turai saboda annobar cutar Corona.

Jaridar NewYork Times ISIS ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar a jaridarta na ‘Al-Naba’ indsa ta shawarci duk mayakanta dake turai, kuma har sun kamu da cutar, toh su yi zamansu a can domin cigaba da yada ta ga kafirai.

KU KARANTA: Ayarin motocin mataimakin shugaba Osinbajo sun gamu da mummunan hatsari a Abuja

Kungiyar ISIS ta hana mayakanta kai hare hare a kasashen turai saboda tsoron Corona

Kungiyar ISIS ta hana mayakanta kai hare hare a kasashen turai saboda tsoron Corona
Source: UGC

“Wannan bala’i wani nau’i ne na azaba da Allah Yake saukar ma duk wanda ya so, don haka wanda bai kamu ba kada ya sake ya shiga yankin da annobar ta watsu, wanda kuma ya kamu kadsa ya fita daga yankin.” Inji ISIS.

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito akwai akalla mutane 110 da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar Iraqi, kasar da burbushin ISIS suka rage, kuma akwai guda 10 daga cikinsu wanda cutar ta kai intiha a kansu.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Amurka, Donald J. Trump ya yi gwaji domin gano ko cewa ya na dauke da cutar nan ta Coronavirus da ta zama annoba yanzu a kasashen Duniya.

Jaridar New York Times ta ruwaito sakamakon wannan gwaji da shugaban na Amurka ya yi, ya nuna cewa bai dauke da cutar. Fox News sun fitar da wannan rahoto ne a Ranar Asabar, 14 ga Watan Maris, 2020.

Ana sa ran ba da dadewa ba, Duniya za ta san halin da Donald Trump ya ke ciki. Tun a baya a lokacin da ya gana da Manema labaran da ke cikin fadar shugaban kasa, Mai girma Donald Trump ya shaida masu cewa garau ya ke jin kansa.

Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa jikinsa bai yi wani zafi ba. Zafin jiki da tari su na cikin alamomin wannan cuta ta Coronavirus da ba a gane kanta ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel