Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa mahaifiyar Gwamna Yahaya Bello rasuwa
Allah ya yi wa Hauwa Bello, mahaifiyar Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi rasuwa. Hajiya Bello ta rasu ne a ranar Lahadi tana da shekaru 101 a duniya.
Sanarwar rasuwar nata yana cikin wani sako mai dauke da sa hannun gwamnan da aka aike wa Premium Times.
Ta rasu ta bar yara, jikoki tattaba kuni da kuma yara da yawa 'yan riko.

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Shugabar wurin aikin mu ta kori ne don na ki yin zina da ita - Matashi
Ga cikakken sanarwar a kasa:
Innalilahi wa inna illaihi raji'un
"A madadin iyalan Alhaji Bello Ipemida Ochi, muna son sanar da rasuwar mahaifiyarmu, Hajia Hauwau Oziohu Bello wacce ta amsa kirar ubangiji a yammacin yau bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Za a yi jana'izarta a yau a gidanta da ke Nagazi, karamar hukumar Okene bisa koyarwa addinin musulunci.
Kafin rasuwar ta, tana da shekaru 101 kuma ta rasu ta bar 'ya'ya, jikoki, tattaba kunni masu yawa da yara na riko.
Sanarwa daga Alhaji Yahaya Adoza Bello (Ɗan ta)
Gwamnan jihar Kogi a madadin iyalan ta."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng