Tube rawanin Sanusi: AGF Malami ya yi zazzafan martani

Tube rawanin Sanusi: AGF Malami ya yi zazzafan martani

- Antoni janar din kasar nan kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya ce bashi da hadi da sauke rawanin tsohon sarkin Kano

- Malami ya sanar da hakan ne a wata takarda da ya fitar a Abuja a ranar Lahadi ta hannun Dr Umar Gwandu

- Ministan ya sanar da cewa maganar na gaban kotu don haka ba zai yi tsokacin komai a kai ba

Antoni janar din kasar nan kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya ce bashi da hadi da sauke rawanin tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II da kuma mayar dashi zuwa jihar Nasarawa.

Malami ya sanar da hakan ne a wata takarda da ya fitar a Abuja a ranar Lahadi ta hannu Dr Umar Gwandu, mataimaki na musamman gare shi ta fannin yada labarai.

Tube rawanin Sanusi: AGF Malami ya yi zazzafan martani
Tube rawanin Sanusi: AGF Malami ya yi zazzafan martani
Asali: Twitter

DUBA WANNNAN: Addu'ar da mahaifiyar Sanusi II ta zazzaga masa yayin da ta ziyarce shi (Bidiyo)

“Maganar sauke rawanin basaraken an mika ta gaban shari’a kuma ana duba ta. Don haka ba zanyi tsokaci a kan maganar da ke gaban kotu ba.”

Sanusi ya yi ikirarin cewa Antoni janar din jihar Kano, Ibrahim Mukhtar da kuma Antoni janar din kasa ne suka ba hukumar jami’an tsaro ta fararen kaya da ‘yan sanda umarnin tsaresa.

Kamfani Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, tubabben sarkin Kano din a ranar Alhamis ya maka sifeta janar din ‘yan sanda Najeriya, Mohammed Adamu, Darakta janar din DSS, Yusuf Bichi, kwamishinan shari'ar jihar Kano, Ibrahim Mukhtar da ministan shari'ar Najeriya, Abubakar Malami a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja a kan zarginsu da tsaresa .

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel