Yadda diyar Sanusi tayi hasashen tube rawanin mahaifinta

Yadda diyar Sanusi tayi hasashen tube rawanin mahaifinta

'Yan Najeriya sun sha mamaki a lokacin da aka tubewa babban sarki na Kano, Malam Muhammadu Sanusi II rawani tare da maye gurbinsa da dan wanda ya gada, Aminu Ado Bayero. Duk da alakar gwamnan da sarkin ta dade da yin tsami, babu wanda ya taba hasashen hakan za ta faru.

A shekarar 2017, diyar Sanusi II, Shahida, ta yi wani jawabi a taron farko na tunawa da 'yan matan Chibok da aka sace a garin Abuja, inda ta ce akwai yiwuwar tube rawanin mahaifinta.

A jawabinta, ta jaddada cewa duk da burin mahaifinta na ci gaba da sarautar Kano har zuwa karshen rayuwarsa, ba zai kuwa zuba ido ya kalla rashin dacewar lamurra ba.

Ta ce: "Mahaifina baya iya zama babu gwagwarmaya. Yana gwagwarmaya don ci gaba, 'yanci da daidaituwa. Don haka, wadanda suke tunanin sun san mahaifina su sani, ba zai taba yin shiru saboda wata barazana ba. Ya rasa mukaminsa na gwamnan babban bankin Najeriya.

Yadda diyar Sanusi tayi hasashen tube rawanin mahaifinta
Gimbiya Shahida
Asali: Facebook

Ban sani ba ko zaku tuna yana cewa 'zaku iya dakatar dani, amma ba zaku iya dakatar da gaskiya ba. A duk lokacin da aka tunkareka da zabi a kan daidai da kuma sanannen abu, dole ne kayi abinda ya zama daidai.'

DUBA WANNAN: Addu'ar da mahaifiyar Sanusi II ta zazzaga masa yayin da ta ziyarce shi (Bidiyo)

"Ya koya mana kuma nasan ba zai damu ba koda zai zama sarkin da yafi kowanne rashin suna a kan yana fadin gaskiya. A bangaren mulki kuwa, yana cewa Ubangiji ne ya bashi kuma shi zai iya karba. Ina da tabbacin zai so dawwama a sarautar har sai karshen rayuwarsa amma na san ba zai sadaukar da komai don hakan ba."

Kamar yadda tace, ta fara kaunar nagarta ne lokacin da aka ba mahaifinta lambar yabo ta nagarta. Shahida ta kara da cewa: "Kawai yin abinda ya dace ne ya kamata komai rintsi. Na san idan aka bukaci mahaifina ya zaba tsakanin karagar mulki da gaskiya, toh ba shakka zai bar mulkin. Ya cika burinsa na gadar kakanninsa kuma har yanzu shine dai ma'aikacin bankin na kuma gwamnan babban bankin Najeriya. A matsayinsa na sarki, shi din ne dai koda kuwa saukesa aka yi. Ba zai taba yin shiru ba ko a mulki ko babu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel