Kisan kiyashin da ake yiwa Musulmai a Delhi ya sanya su barin gidajensu don su tsira da rayukansu

Kisan kiyashin da ake yiwa Musulmai a Delhi ya sanya su barin gidajensu don su tsira da rayukansu

Imran Khan, wani matashi mai shekaru 30 a duniya, bayan dawowa daga aikin leburanci a ranar 24 ga watan Fabrairu, sai ya ci karo da 'yan banga a yankin arewa maso gabashin Delhi

"Sun fara tambayata sunana domin su tabbatar da ni Musulmi ne ko kuma Hindu ne," ya sanar da CBS News. Yana fadar sunanshi, wanda kowa ya san sunan a yankin kudancin Asiya na Musulmai ne, sai kawai suka fara dukan shi da karafuna.

"Na fara basu hakuri, amma basu saurare ni ba. Suna ta dukana suna yi mini dariya, inda wasu daga cikinsu suka cinye dan kayan marmarin dana sayowa yarana."

Sun yiwa Khan dukan da ko iya motsawa bayayi, lokacin da ya dan farfado ya ganshi a wani wuri cikin ruwa da igiya a daure a wuyanshi.

"Ina jin sunyi tunanin na mutu ne ya sanya suka jefa ni cikin ruwan," ya sanar da CBS News a sansanin 'yan gudun hijira dake Mustafabad, inda ya koma don samun matsugunni. Khan ya nuna irin raunikan da suka ji masa, inda ya ce: "Allah ne kawai ya ceto rayuwata."

KU KARANTA: Kasar Amurka ce ta kawo mana cutar Coronavirus don ta bata sunan mu a idon duniya - Zargin kasar China

Khan yana daya daga cikin mutanen da suka kafa sansanin gudun hijira daga cikin wadanda suka gudo daga birnin na Delhi a watan da ya gabata. Wannan rikici dai a yanzu yayi sanadiyyar mutuwar mutane 53 da kuma sama da mutane 200 da suka ji muggan raunika.

Wannan lamari dai ya samo asali ne tun lokacin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kai ziyara kasar Indiya, inda wasu da suke kalubalantar hukuncin kundin tsarin mulkin kasar na nuna wariya da kuma canja tsarin zama dan kasa akan Musulmai suka fara rikici da wadanda suke son wannan doka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: