Kwankwaso: Ina farin ciki domin wadanda suka yi garkuwa da Sanusi sun sake shi

Kwankwaso: Ina farin ciki domin wadanda suka yi garkuwa da Sanusi sun sake shi

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ya yi farin ciki saboda wadanda suka yi garkuwa da Muhammadu Sanusi II tsohon sarkin Kano sun sako shi.

Kwankwaso ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke magana da manema labarai a filin tashi da saukan jirage na Nnamdi Azikwe inda ya gana da Sanusi kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kwankwaso ya ce, "Ina farin ciki domin wadanda suka yi garkuwa da shi sun sako shi yanzu. Yanzu yana da 'yancinsa kuma zai tafi Legas, mun yi murna da hakan."

Kwankwaso: Ina farin ciki domin wadanda suka yi garkuwa da Sanusi sun sake shi
Kwankwaso: Ina farin ciki domin wadanda suka yi garkuwa da Sanusi sun sake shi
Asali: UGC

DUBA WANNAN: UNIZIK ta dage bawa Sanusi digirin karramawa

A shekarar 2014, Kwankwaso ne ya nada Sanusi a matsayin sarkin Kano na 14 duk da cewa akwai wasu da ba su so hakan ba.

Da ya ke kare nadin da ya yi a wannan lokacin, Kwankwaso ya ce: "Abin takaici ne wasu makiya Kano sun yi kokarin saka siyasa cikin lamarin. Mai martaba Sanusi yana cikin wadanda aka mika sunayensu kuma sunansa ne a farko."

Bayan an cire Sanusi II daga kujerar sarautar Kano, jagoran na tafiyar Kwankwasiyya ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bayar da umurnin tsige Sanusi.

Ya kara da cewa, "Wasu shugabanni a nan gwamnatin jihar Kano su kansu suna cewa an basu umurnin cire sarkin ne."

"Shi (Shugaba Muhammadu Buhari) ne ya basu umurnin su cire sarkin. Kamar yadda muka gani a nan Kano, duk abinda Buhari ya saka hannu ciki yana lalata shi."

Kwankwaso ne ya mika wa Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya yi aiki a matsayin mataimakinsa mulkin jihar Kano a lokacin da ya mulki jihar.

Sai dai daga bisani alakar da ke tsakaninsu da yi tsami.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel