Yanzu-yanzu: Sanusi II ya isa Legas (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Sanusi II ya isa Legas (Hotuna)

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya isa filin tashi da saukan jirage na Murtala Mohammed da ke Legas a daren jiya daga Abuja bayan ya taso daga filin tashin jiragen sama na Nnamdi Azikwe na Abujan.

Ya baro Abuja misalin karfe 10.14 na daren jiya Juma'a a wata jirgin haya ta Quits Aviation.

Rahotanni sun bayyana cewa ya isa Legas misalin karfe 11.35 na dare kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa matansa da 'ya'yansa tare da masoya da masu masa fatan alheri sun isa Legas domin tarbarsa.

Yanzu-yanzu: Sanusi II ya isa Legas

Yanzu-yanzu: Sanusi II ya isa Legas
Source: Twitter

DUBA WANNAN: UNIZIK ta dage bawa Sanusi digirin karramawa

Sanusi ya tafi filin tashi da saukan jirage na Abuja tare da gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai.

Yanzu-yanzu: Sanusi II ya isa Legas (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Sanusi II ya isa Legas (Hotuna)
Source: Twitter

Tun kafin ya isa filin tashin da sauka na jiragen wasu masoyansa sun taru suna jirarsa tare da ma'aikata filin tashin jiragen.

Misalin karfe 8 na dare, wata tawaga ta iso cikin wata mota kirar SUV tare da dansa Muhammad.

Lokacin da ya isa misalin karfe 10 na dare, mutane da dama sun tarbe shi suna masa kirari da cewa 'Allah ya rufa maka asiri'.

Wani mutum da aka ce dan uwan Sanusi ne, Shamsudeen Zubairu Usman ya shaidawa Daily Trust Saturday ya ce iyalansa sun yi murnar hukuncin da kotu ta yanke kuma suna jiransa a Legas.

Ya ce, "Hukuncin kotun ya nuna cewa kotu tana aiki a Najeriya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel