Buhari ya fitar da naira biliyan 285 domin aiwatar da manyan ayyuka a Najeriya

Buhari ya fitar da naira biliyan 285 domin aiwatar da manyan ayyuka a Najeriya

Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta saki kimanin naira biliyan 285 don gudanar da manyan ayyuka dake zube a cikin kasafin kudin shekarar 2020.

Punch ta ruwaito ministan kudi, kasafin kudi da tsare tsare, Zainab Shamsuna Ahmad ce ta bayyana haka a babban birnin tarayya Abuja yayin da take ganawa da manema labaru inda ta ce sun saki kudin ne a ranar Talata.

KU KARANTA: Hukumar kula da shige da fice ta kammala shirin daukan matasan Najeriya aiki

Ministar ta bayyana haka ne jim kadan bayan ganawar da ta yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa.

“Ma’aikatu da hukumomin dake kula da manyan ayyuka da suka hada da ma’aikatar sufuri, ma’aikatar ayyuka da gidaje da kuma ma’aikatan kula da yankin Neja Delta ne suka samu kudaden.” Inji ta.

Minsita Zainab ta kara da cewa gwamnatin Najeriya ta kara sakin dala miliyan 220 a matsayin kudin da zata biya domin gudanar da aikin layin dogo a Najeriya, kuma ma’aikatar sufuri ce ta amshi kudin.

A wani labarin kuma, kwamitin gudanarwa dake kula da hukumar tsaro ta farin kaya, Civil Defence, hukumar kashe gobara, Fire Service da hukumar kula da shige da fice, Immigration, watau CDFIB, ta amince da bukatar hukumar kula da shige da fice na daukan sabbin ma’aikata a shekarar 2020.

Jami’i magana da yawun hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, NIS, Sundaye James ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a babban birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a, inda yace kwamitin gudanarwa a karkashin jagorancin Ministan cikin gida Rauf Aregbesola ne ta amince da daukan aikin.

“Za’a dauki makonni hudu ana hidimar daukan aikin daga ranar da aka sanar a hukumance, don haka ake kira ga jama’a su yi amfani da wannan dama domin su nemi aikin nan.” Inji shi.

Haka zalika Sunday ya gargadi jama’a daga shiga yanar gizon da ba na hukumar ba da nufin neman aikin, inda ya bayyana sahihin adireshin yanar gizon hukumar kamar haka www.nisrecruitment.org.ng.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel