Hotunan ganawar Sanusi II da El-Rufai a garin Awe

Hotunan ganawar Sanusi II da El-Rufai a garin Awe

A yau Juma'a 13 ga watan Maris ne Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya tafi garin Awe na jihar Nasarawa domin ya ziyarci tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

An mayar da Sanusi II garin Awe na daga Loko bayan Gwamna Ganduje na jihar Kano ya sauke shi daga kujerarsa ta sarauta.

Bayan saukar sarkin, gwamnan na jihar Kaduna ya masa tayin mukamai biyu a gwamnatinsa a jami'ar jihar wato KASU da kuma KADIPA.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Sanusi ya sanar da amincewa da karbar mukamin ne cikin wata sanarwa mai dauke da saka hannun hadimin Gwamna El-Rufai, Muyiwa Adekeye a ranar Laraba 11 ga watan Maris.

Gwamnan ya mika godiyarsa ga tsohon sarkin saboda cigaba da bayar da goyon bayansa domin ganin jihar ta Kaduna ta cinma burinta.

DUBA WANNAN: Sarkin Loko ya bayyana abinda suka tattauna da Sanusi II a daren da ya kwana a garinsa

A wani rahoton kun ji cewa babban kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja a ranar Juma'a ta bayar da umurnin sakin tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II daga inda aka tsare shi a garin Awe na jihar Nassarawa bayan an cire daga kan mulki a ranar Litinin.

Mai shari'ar Anwuli Chikere ne ta bada da umurnin haka sakamakon bukatar da shugaban lauyoyin sa, Lateef Fagbemi (SAN) ya shigar a ranar Juma'a.

Kotun ta ce a mika takardan umurnin sakin Sanusi da dukkan hukumomin da suka tsare da shi.

Bayan hukuncin kotun, tsohon Sarki Sanusi II da iyalansa za su kama hanya zuwa jihar Legas inda zai cigaba da zama tare da iyalansa a halin yanzu.

Tsohon sarki Sanusi II ne ya jagorancin sallar Juma'a na yau 13 ga watan Maris a garin inda matasa da al'umma masu yawa suka hallarci sallar.

Gwamna El-Rufai yana daga cikin wadanda suka yi sallar Juma'ar a garin na Awe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel