Diyar Sanusi II ta bayyana inda mahaifinta ke son a kai littatafansa

Diyar Sanusi II ta bayyana inda mahaifinta ke son a kai littatafansa

- Khadija Yusra Sanusi, diyar tsohon sarkin Kano, ta ce mahaifinta ya so ne jami'ar Bayero da ke Kano ta gaji litattafansa

- Dakin karatunsa ya jawo cece-kuce ko bayan kuwa da aka saukesa daga sarautar Kano yayin da jama'a ke tambayar makomar littatafansa

- A yayin tsokaci a kan littatafan, Yusra ta ce mahaifinta na so daliban jami'ar Bayero ne su amfana da littatafan

Khadija Yusra Sanusi, diyar tsohon sarkin Kano, ta ce mahaifinta ya so ne jami'ar Bayero da ke Kano ta gaji litattafansa.

An tube rawanin Muhammadu Sansui II ne a ranar Litinin. A halin yanzu kuwa yana garin Awe da ke jihar Nasarawa inda ya samu mafaka

Dakin karatunsa ya jawo cece-kuce ko bayan kuwa da aka saukesa daga sarautar Kano yayin da jama'a ke tambayar makomar littatafansa.

A ranar Alhamis, Mujitaba Abba, sakataren fadar wanda yayi murabus bayan sauke dan uwansa daga sarautar, ya bayyana cewa an kwashe littatafan daga fadar.

Diyar Sanusi II ta bayyana inda mahaifinta ke son a kai littatafansa
Diyar Sanusi II ta bayyana inda mahaifinta ke son a kai littatafansa
Asali: UGC

KU KARANTA: Yadda wani matashi ya kaiwa Buhari damka a Kebbi (Bidiyo)

An gano cewa wannan dakin karatun zai kai darajar miliyan dari biyu kuma yana da littatafai sama da 40,000 a cikinsa.

"Mai martaba ya matukar shiga damuwa a kan makomar dakin karatunsa wanda zai kai darajar naira miliyan 200. Don haka ni da 'yar uwata muka tsaya don tabbatar da cewa an kwashe dukkan littatafan," Abba yace.

"Sai da muka ajiye bacci na tsawon kwanaki biyu kafin mu iya aiwatar da hakan. Da kaina na dinga siyo littatafan kuma zan iya sanar da cewa sun haura na miliyan 200."

A yayin tsokaci a kan littatafan, Yusra ta ce mahaifinta na so daliban jami'ar Bayero ne su amfana da littatafan.

"A hankali dai, mahaifina ya tsara yadda daliban BUK zasu gaji littatafan ta yadda fadar za ta taka rawar gani wajen habaka ilimi," Yusra ta rubuta a shafinta na twitter.

"Littatafai wani mabudi ne na ilimi kuma damar samun littatafai kala-kala baiwa ce."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel