Yadda wani matashi ya kaiwa Buhari damka a Kebbi (Bidiyo)
- A jiya ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Kebbi don halarta kashin karshe na gasar kamun kifi na Argungun
- Manyan jami’an gwamnati karkashin jagorancin Gwamna Atiku Bagudu be suka tarbi shugaban a filin jirgin sama
- Wani bawan Allah ne ya kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari damka a yayin da yake daukar hoto tare da wasu manyan jiga-jigan gwamnati
A jiya ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Kebbi don halarta kashin karshe na gasar kamun kifi na Argungun da aka yi a jihar Kebbi.
Manyan jami’an gwamnati karkashin jagorancin Gwamna Atiku Bagudu be suka tarbi shugaban a filin jirgin sama. Da farko gwamnatin tarayya a ranar Alhamis, 12 ga watan Maris, ta kaddamar da bikin kamun kifi na Argungu a Abuja.
Amma kuma sai wani abu mai cike da mamaki ya faru a yayin da shugaban kasar ke wajen.
Wani bawan Allah ne ya kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari damka a yayin da yake daukar hoto tare da wasu manyan jiga-jigan gwamnati.
Wannan lamari kuwa ya kawo hargitsi a wajen don da gaggawa jami'an tsaro suka damki mutumin tare da fitar da shi daga wajen.
KU KARANTA: Anyi gudun fanfalaki a wajen wani cin abinci bayan wani dan kasar China da ake tunanin yana da Coronavirus yaje wajen
A yayin kaddamar da bikin baje kolin noman da aka yi a Abuja, shugaban kasar wanda ya samu wakilcin ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed a Abuja, ya ce samar da kafar amfani da kayayyakin gida a bikin wannan shekarar ya yi bayanin manufar gwamnati kan amfani da kayayyakin da aka sarrafa a gida Najeriya.
Ya kara da cewa a shirye gwamnatin tarayya ta ke ta yi amfani da masana’antar motoci da ka iya samar da biliyoyin daloli ga kasar a duk shekara.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng