Matawalle ya bayyana dalilin dawowar sabbin hare-hare a Zamfara

Matawalle ya bayyana dalilin dawowar sabbin hare-hare a Zamfara

- Gwamnatin jihar Zamfara ta zargi rashin tsare iyakokin kasar nan da taimakawa wajen sabbin hare-haren 'yan ta'addan da tsageru a jihar

- Gwamna Bello Mohammed ya jajanta yadda tsagerun suka kutsa kauyukan Gummi, Bukkuyum, Anka da Maru da ke jihar Zamfara

- Gwamna Mohammed ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta shirya tsaf don kawo karshen ta'addanci a jihar

Gwamnatin jihar Zamfara ta zargi rashin tsare iyakokin kasar nan da taimakawa wajen sabbin hare-haren 'yan ta'addan da tsageru a jihar.

Gwamna Bello Mohammed ya jajanta yadda tsagerun suka kutsa kauyukan Gummi, Bukkuyum, Anka da Maru da ke jihar Zamfara. Ya kwatanta lamarin da mara dadi kuma abun alhini.

A wata takarda da Zailani Bappa, mai bada shawara ta musamman ga gwamnan a kan wayar da kai, yada labarai da sadarwa, yasa hannu, Gwamna Mohammed ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta shirya tsaf don kawo karshen ta'addanci a jihar.

An gano cewa, lamurra na kara tsamari tsakanin 'yan bindigar jihar da kuma mahakan albarkatun kasa dake jihar.

Matawalle ya bayyana dalilin dawowar sabbin hare-hare a Zamfara
Matawalle ya bayyana dalilin dawowar sabbin hare-hare a Zamfara
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Hotunan bindigu, alburusai, kudi da kwayoyi da rundunar 'yan sanda ta kama tare da masu garkuwa da mutane a Abuja

A wani labari na daban, a ranar Laraba ne rundunar 'yan sanda a Abuja ta yi bajakolin masu garkuwa da mutane da 'yan fashi da makami da jami'an tawagar yaki da fashi da makami (SARS) suka kama a jihohi daban - daban.

Daga cikin miyagun kayayyakin da aka samu a wurin masu laifin akwai bindigu 30 da suk hada da AK47 da kuma wasu na gida, carbi 1520 na alburusai, miyagun kwayoyi da kuma makudan takardun kudi.

Yayin bajakolin masu laifin, wasu daga cikinsu sun nuna yadda suke boye bindigu a jikin babur da mota yayin da za su fita ofireshon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel