An fara: Gwamnan Ekiti ta tuhumci Sarakuna 11 da laifin rashin biyayya

An fara: Gwamnan Ekiti ta tuhumci Sarakuna 11 da laifin rashin biyayya

Gwamnatin jihar Ekiti ya aika wasikun tuhuma ga Sarakunan gargajiya masu matsayi na daya 11 kan zargin rashin biyayya ga gwamnatin jihar da jagorancin majalisar sarakunan jihar.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta bada rahoton cewa an aikewa sarakunan 11 wasikar mai take “Rashin halartan tarukan iha da majalisar sarakuna“ ranar Laraba kuma an bukacesu su yi bayani nan da kwanaki uku.

Wasikar ta tuhumci sarakunan gargajiyan da laifin kin halartan ganawar sarakunan jihar na wata-wata na tsawon watanni 8 tun watan Agusta, 2019.

NAN ta samu labarin cewa wannan mataki da gwamnatin Ekiti ta dauka ya razana Sarakunan ranar Alhamis inda wasu suka ce gwamnan jihar na shirin dakatad da su ko kwance musu rawani ne dubi ga irin abinda ya faru a jihar Kano.

Za ku tuna cewa rikici ya kunno kai tsakanin sarakunan jihar Ekiti ne lokacin da gwamna Fayemi ya nada Alawe of Ilawe Ekiti matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar.

Hakan bai yiwa wasu sarakuna dadi ba musamman wadanda suke ganin wanda aka nada bai cancanci kujerar ba kuma yana kasa da su.

Saboda haka, sai suka daina halartan taron majalisar Sarakunan jihar da ake wata-wata.

Mun kawo muku rahoton cewa a ranar Litinin, gwamnatin jihar Kano ta tsige mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu.

Hadimin gwamnan Kanon kan sabbin kafafen yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 9 ga watan Maris, 2020.

Yace: "Majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da tsige sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II."

Hakazalika, sakataren gwamnatin jihar, Usman Alhaji, ya saki jawabi kan dalilin da yasa gwamnatin jihar ta tunbuke sarkin Kano daga kujerar

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel