Yanzu-yanzu: ASUU ta cimma matsaya da gwamnatin tarayya kan IPPIS

Yanzu-yanzu: ASUU ta cimma matsaya da gwamnatin tarayya kan IPPIS

Gwamnatin Najeriya ta cimma matsaya da malaman jami'o'in kasar inda za ta gwamatsa tsarin bin diddigi na jami'o'i (UTAS) cikin tsarin hadadden bayannan albashin ma'aikata na IPPIS.

IPPIS wani manhajja ce ta gwamnatin tarayya da aka wajabta wa dukkan ma'aikatun gwamnati amfani da shi musamman domin tantance albashin ma'aikatan kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

ASUU ta ki amincewa da IPPIS ga malaman jami'a inda ta ce akwai wasu abubuwa da ke tafiya a jami'o'i da ba ayi la'akari da su ba a cikin manhajjar. Kungiyar ta malaman jami'an ta kirkiri nata manhajjar mai suna UTAS wanda ta ke son gwamnatin tarayyar ta rika yi wa malamai amfani da shi.

Yanzu-yanzu: ASUU ta cimma matsaya da gwamnatin tarayya kan IPPIS
Yanzu-yanzu: ASUU ta cimma matsaya da gwamnatin tarayya kan IPPIS
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sarkin Loko ya bayyana abinda suka tattauna da Sanusi II a daren da ya kwana a garinsa

Ministan Kwadago na kasar, Chris Ngige ya sanar da cewa bangarorin sun cimma matsaya bayan sun kwashe awanni hudu suna tattaunawa.

Mista Ngige ya ce bangarorin biyu za su sake haduwa a ranar Litinin bayan tawagar ASUU ta sake tattaunawa da majalisar zartarwar ta (NEC).

A jawabinsa, Shugaban ASUU na kasa, Biodun Ogunyemi ya ce majalisar zartarwar ta kungiyar za ta yi bitan sharuddan shigar da UTAS cikin IPPIS.

Sai dai kawo yanzu dukkan bangarorin biyu ba su bayyana wa manema labarai sharudan ba.

A ranar Litinin ne ASUU ta fadawa mambobin ta na jami'o'in tarayya a kasar su fara yajin aikin yi na sati biyu saboda matakin da gwamnati ta dauka ne tsayar da albashin watan Fabrairu na malaman da ba su yi rajista ba su shiga tsarin IPPIS ba.

Taron da aka yi na ranar Alhamis ita ce ta farko tun bayan fara yajin aikin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel