UNIZIK ta dage bawa Sanusi digirin karramawa

UNIZIK ta dage bawa Sanusi digirin karramawa

Jami'ar Nnamdi Azikwe da ke Awka a jihar Anambra a ranar Alhamis, ta dage digirin karramawa da a baya ta yi shirin ba wa tubabben sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Shugaban jami'ar Farfesa Charles Esimone ne ya sanar da dage bayar da digirin yayin bikin yaye dalibai karo na 14 na jami'ar.

Esimone ya ce an dage bayar da digirin ne saboda abinda halin da tsohon sarkin ya tsinci kansa a yanzu.

Shugaban jami'ar ya ce za a bawa Sanusi digirin na karramawar nan gaba idan za a sake bikin yayen daliban.

UNIZIK ta dage bawa Sanusi digirin karramawa

UNIZIK ta dage bawa Sanusi digirin karramawa
Source: UGC

DUBA WANNAN: Sarkin Loko ya bayyana abinda suka tattauna da Sanusi II a daren da ya kwana a garinsa

Shugaban jami'ar ya ce, "Za a bawa tsohon sarkin digirin karramawar a nan gaba yayin bikin yaye daliban.

"Majalisar jami'ar ta amince da bawa tsohon sarki Muhammadu Sanusi II digirin."

Za a karrama Sanusi ne da digirin Dakta ta girmamawa a fanin takaita asara.

A ranar Litinin ne gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sauke Sanusi daga kujerar sarautar Kano ya kuma tura shi jihar Nasarawa inda aka tsare da shi.

Suaran 'yan Najeriya biyu da aka karrama a wurin bikin yayen daliban da digirin sune Cif Innocent Chukwuma, wanda shine shugaban kamfanin motocci ta Innosson Motors, Nnewi da Cif Daniel Chukwudolue na kamfanin Dozie Oil.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel