Yanzu-yanzu: Sanusi II ya maka IGP, shugaban DSS, kwamishinan shari'ar Kano da ministan shari'ar Najeriya a kotu

Yanzu-yanzu: Sanusi II ya maka IGP, shugaban DSS, kwamishinan shari'ar Kano da ministan shari'ar Najeriya a kotu

Tsohon sarkin Kano, Lamido Sanusi II, ya mika korafi gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a kan bukatar ta bada umarnin sakinsa bayan tsigesa da aka yi daga karagar mulkin masarautar Kano.

An dauke Sanusi zuwa garin Awe ne da ke jihar Nasarawa kuma tuni aka tsaresa a wani gida da ke garin bayan gwamnatin jihar Kano ta tube masa rawani a ranar Litinin da ta gabata.

Lauyoyinsa wadanda suka samu shugabancin Lateef Fagbemi, a ranar Alhamis sun shigar dakarara mai lamba FHC/ABJ/CS/357/2020 a gaban babbar kotun tarayyar da ke Abuja, jaridar The Punch ta ruwaito.

Ya roki kotun da ta bada uamrani sakin wanda yake karewa tare da dawo masa da yancinsa na zuwa inda ya ga dama da kuma mu’amala da jama’a a Najeriya amma banda jihar Kano.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa wadanda ake karar sun hada da shugaban ‘yan sandan Najeriya, shugaban hukumar ‘yan sandan farin kaya ta Najeriya, kwamishinan shari’ar jihar Kano da kuma ministan shari’ar Najeriya.

Yanzu-yanzu: Sanusi II ya maka IG, shugaban DSS, kwamishinan shari'ar Kano da ministan shari'ar Najeriya a kotu

Yanzu-yanzu: Sanusi II ya maka IG, shugaban DSS, kwamishinan shari'ar Kano da ministan shari'ar Najeriya a kotu
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Sarkin Loko ya bayyana abinda suka tattauna da Sanusi II a daren da ya kwana a garinsa

Ya roki kotun da ta bada uamrani sakin wanda yake karewa tare da dawo masa da yancinsa na zuwa inda ya ga dama da kuma mu’amala da jama’a a Najeriya amma banda jihar Kano.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa wadanda ake karar sun hada da shugaban ‘yan sandan Najeriya, shugaban hukumar ‘yan sandan farin kaya ta Najeriya, kwamishinan shari’ar jihar Kano da kuma ministan shari’ar Najeriya.

Idan zamu tuna, a jiya ne Shugaban lauyoyin tubabben sarkin Kano, Abubakar Balarabe Mahmoud, ya yi bayanin yadda Malam Muhammadu Sanusi II da iyalansa suna fuskanci cin zarafi bayan an tube masa rawaninsa.

Balarabe Mahmoud, tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya, ya ce kafin Sanusi ya samu wasikar tube masa rawani, an samu hargitsi a sashin iyalan mai martaban domin kuwa wasu mutane da bai dace ba sun so shiga sashin iyalan mai martaban.

Babban lauyan ya ce, "Wannan lamarin yayi kamari don har barkonon tsohuwa aka watsa. Hankula sun kwanta ne bayan da wadannan mutanen suka janye daga yunkurin shiga sashin iyalan mai martabar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel