Yanzu-yanzu: Gwamnan Nasarawa, Sarkin Lafiya sun ziyarci Sanusi a Awe

Yanzu-yanzu: Gwamnan Nasarawa, Sarkin Lafiya sun ziyarci Sanusi a Awe

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, tare da Sarkin Lafiya da Sarkin Awe sun kaiwa tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ziyara a gidansa ke Awe a ranar Alhamis, 12 ga Febrairu, 2020.

Gwamnan, wanda ya dira gidan misalin karfe 5:10 tare da Mai martaba Sarkin Lafiya, Sidi Dauda Bage, da sarkin Awe, Alhaji Isa Abubakar Umar II.

Wannan ziyarar da gwamnan yayi ya karyata rahotannin cewa an dauke tsohon Sarkin daga Awe zuwa Legas.

Yanzu-yanzu: Gwamnan Nasarawa, Sarkin Lafiya sun ziyarci Sanusi a Awe

Yanzu-yanzu: Gwamnan Nasarawa, Sarkin Lafiya sun ziyarci Sanusi a Awe
Source: Facebook

Rahotanni sun tabbatar da gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya kai ma amininsa, tsohon sarkin masarautar Kano, Muhammadu Sunusi II ziyara a sabon gidansa da yake zaman hijira a a Awe, jahar Nassarawa.

Daily Trust ta ruwaito wasu majiyoyi daga hukumomin tsaro ne suka tabbatar mata da ziyarar gwamnan, inda suka ce Gwamna El-Rufai ya tashi daga Kaduna ne da safiyar Alhamis, 12 ga watan Maris ya nufi Awe don ganawa da Sarki mai murabus.

Idan za’a tuna a ranar Laraba ne El-Rufai ya nada Malam Muhammadu Sunusi a matsayin uban jami’ar jahar Kaduna, KASU.

Wannan nadi ya biyo bayan nadin da gwamnatin jahar Kaduna ta yi ma Sunusi a ranar Talata, 10 ga watan Maris ne inda ta nada shi mukamin mataimakin kwamitin gudanarwa na hukumar zuba hannun jari a jahar Kaduna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel