Yanzu-yanzu: Buhari ya amince da zaman majalisar zartarwar APC babu Oshiomole ba

Yanzu-yanzu: Buhari ya amince da zaman majalisar zartarwar APC babu Oshiomole ba

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da zaman majalisar zartarwa jamiyyar All Progressives Congress APC da aka shirya yi ranar Talata 17 ga Maris, 2020 ba tare da shugabasu Adams Oshiomole ba. Daily Trust ta ruwaito.

Daya daga cikin majiyar ya bayyanawa DT cewa an shirya zaman ne da goyon bayan shugaban kasa kuma zai halarta.

Yace “Da goyon bayansa za a yi. Saboda haka tambaya cewa zai halarta ko ba zai halarta bata lokaci ne.“

Rahotanni sun bayyana cewa an shirya zaman majalisar zartarwar jamiyyar ne saboda yanke shawarar tunbuke Adams Oshiomole.

KU KARANTA Dan Italiyan da ya kawo Coronavirus Najeriya ya samu sauki, za'a sallameshi - Ministan Lafiya

Zaku tuna cewa a ranar Larabar makon da ya kamata, babbar kotun tarayya dake Abuja ta dakatad da Oshiomole matsayin shugaban jamiyyar APC.

A yanzu haka, Adams Oshiomole na shirin garzayawa kotu domin hana zaman majalisa zartarwar.

Wannan zaman ya kawo rabuwar kai cikin kwamitin gudanarwar jamiyyar. Daga cikin wadanda ke goyon bayan Adams Oshiomole sune kakakin APC, Malam Lanre Isa-Onilu da Babatunde Ogala (Mai bada shawara kan lamuran sharia).

Daya daga cikin mambobin majalisar da aka sakaye sunansa ya bayyana cewa masu goyon bayan Oshiomole na iyakan kokarinsu wajen tabbatar da cewa zaman bai yiwu ba.

Yace “Suna ta neman hukuncin kotu domin hana zaman NEC. Ba sa son a yi zaman saboda suna tsoron idan akayi za a cire Oshiomole.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel