Burin marigayi sarki Ado Bayero ya cika - Sarki Aminu

Burin marigayi sarki Ado Bayero ya cika - Sarki Aminu

Aminu Ado Bayero, sarkin Kano ya ce burin mahaifinsu ya cika da yadda ya zama sarkin Kano. Sarkin ya sanar da hakan ne a ranar Laraba a gidan gwamnatin jihar Kano bayan shi da dan uwansa sun karba wasikar kama aiki daga Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano.

Bayero ya samu hayewa karagar mulkin jihar Kano ne bayan tube rawanin Muhammadu Sanusi II, a yayin da dan uwansa, Nasiru Bayero ya maye gurbinsa a masarautar Bichi.

Mahaifinsu, Ado Bayero ya yi shekaru 53 a kan karagar mulkin masarautar Kano kafin ya rasu a 2014.

Sarkin ya ce mahaifinsu ya koya musu hakuri, biyayya da kuma bin dokoki.

"Muna godiya ga Allah da kuma hanyar da kakanninmu suka bi. Muna fatan Allah yayi musu rahama kuma ya hada mu a aljanna," ya ce.

Kamar yadda yace, "Ya tabbatar mana da cewa hakuri na kaiwa ga nasara. A halin yanzu mun ga darasi a bayyane. Ina kira ga jama'a da su ji tsoron Allah kuma su so juna don kawo ci gaba ga masarautar, jihar Kano da kuma Najeriya."

Burin marigayi sarki Ado Bayero ya cika - Sarki Aminu

Burin marigayi sarki Ado Bayero ya cika - Sarki Aminu
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya zubar da hawaye yayin karbar takardar kama aiki

"Ya horemu da mu kasance masu adalci ga jama'a don ubangiji ya ji kan mu da rahama a gobe kiyama. A wannan ranar mai cike da tarihi, zan iya cewa burin marigayi mahaifinmu ya cika." Ya kara da cewa.

Idan zamu tuna, a jiya ne Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya mika takardun kama aiki ga Aminu Ado Bayero da Nasiru Ado Bayero a matsayin sabbin sarakunan masarautun Kano da na Bichi.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa an nada Aminu Ado Bayero ne bayan Gwamnan ya tube rawanin Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano a ranar Litinin. Ya kara da nada Nasiru Ado Bayero ne sakamakon gurbin da Aminu Ado Bayero ya bari a masarautar Bichi.

A yayin jawabin Sarkin bayan karbar takardar kama aikin a gidan gwamnatin jihar Kano, ya ce a matsayinsa na Musulmi, ya yadda da kaddara da kuma ikon Allah. Hakazalika Allah baya kuskure ko kadan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel