Anyi gudun fanfalaki a wajen wani cin abinci bayan wani dan kasar China da ake tunanin yana da Coronavirus yaje wajen

Anyi gudun fanfalaki a wajen wani cin abinci bayan wani dan kasar China da ake tunanin yana da Coronavirus yaje wajen

Masu cin abinci a otel din Naivasha sun ranta ana kare bayan wani dan kasar China ya shiga wajen domin ya sayi abinci

A ranar Talatar 11 ga watan Fabrairu, K24 TV ta ruwaito yadda wasu masu cin abinci a wani otel dake Kamere suka ranta ana kare, bayan wani dan kasar China da alamun sa ke nuni da cewa bashi da lafiya ya shiga wajen cin abincin.

"Dan China din kwarai bashi da lafiya, kuma saboda tsoron cutar Coronavirus ya sanya mutane guduwa daga cikin otel din a lokacin da ya shiga," wani wanda lamarin ya faru a gabanshi ya bayyana.

Anyi gudun fanfalaki a wajen wani cin abinci bayan wani dan kasar China da ake tunanin yana da Coronavirus yaje wajen
Anyi gudun fanfalaki a wajen wani cin abinci bayan wani dan kasar China da ake tunanin yana da Coronavirus yaje wajen
Asali: Facebook

A cewar mutumin, mutanen yankin suna zaune cikin tsoro da fargaba tun lokacin da wannan cuta ta Coronavirus ta kunno kai, inda ya bayyana cewa saboda wajen akwai 'yan China da yawa.

KU KARANTA: Wata mata ta fashe da kuka bayan an yi mata kyautar N65,000, bayan shafe shekaru 8 tana talla ba ta tara komai ba

Bayan ma'aikatan lafiya sunje otel din sun tarar da cewa dan China din har ya gama abinda zai yi ya wuce, kuma ma'aikatan otel din basu tambayi ko shi wanene ba.

"An sanar da jami'an cewa akwai wani dan China da yaje otel din da bashi da lafiya, bayan zuwansu wajen sun tarar da ya riga ya tafi, kuma babu wanda ya san daga inda ya zo." Cewar ministan lafiya na Nakuru, Cif Samuel King'ori.

A yankin Suswa, Narok County kuma, mutanen yankin sun bukaci ma'aikatar lafiya da ta dinga mayar da hankali tana bincikar 'yan kasar China da aka ga cewa ba su da lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel