Taka leda: Athletico ta yi ma Liverpool cin raba ni da yaro har gida
Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool dake rike da kambun zakarun nahiyar turai ta kwashi kashinta a hannu bayan kungiyar Atletico Madrid ta lallasa ta a gida a gaban yan kallonta da ci 3-2.
Legit.ng ta ruwaito Atletico ta lallasa Liverpool ne bayan an kara lokacin taka leda sakamakon Liverpool ta fara zura mata kwallo ta hannun dan wasanta Wijnaldum, daga nan ne kuma wankin hula ya kai su dare.
KU KARANTA: Mutuwa ta yi awon gaba da hadiman gwamna guda 3 cikin kwanaki 5
Bayan an shiga lokacin kari ne dan wasan Liverpool Roberto Firmino ya sake zura ma Atletico kwallo, wanda hakan ya samu musu ran samun nasara a wasan da ci 2-1, a filin wasansu na Anfield.
Sai dai da yake masu iya magana na cewa tsiyar nasara sai za shi gida, sai a lokacin da bai wuce saura mintuna 20 a tashi bane sai kungiyar Atletico ta taso da karfinta, inda ta zura ma Liverpool kwallaye 3 ta hannun Llorente da Alvaro Morata.
Daga cikin wadanda suka nuna kansu a cikin wasan akwai mai tsaron ragar Atletico, Jan Oblak, wanda ya cire kwallaye 9 daga ragarsa, yayin da mai tsaron ragar Liverpool Adrian kuma ya kware ma kungiyarsa sakamakon gaza cire hare hare guda ukun da aka kai masa a wasan.
A yanzu dai ta tabbata Atletico ta fatattaki Liverpool zuwa gida, yayin da ita kuma ta tsallake zuwa zagaye nag aba, sai dai har yanzu Liverpool ce kan gaba a gasar firimiya, inda za ta lashe kofin gasar a karo na farko bayan shekaru da dama.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng