Muna da almajirai miliyan biyu a Zamfara - Gwamnatin Zamfara

Muna da almajirai miliyan biyu a Zamfara - Gwamnatin Zamfara

Direktan Kasafin Kudi na jihar Zamfara, Alhaji Hamza Salisu ya ce akwai kimanin almajirai miliyan biyu da yawo a titunan jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Salisu ya bayyana hakan ne a Gusau a wurin wani taro a kan kare hakkin yara da cigaban su da Save the Children International ta shirya.

Salisu ya ce, "Bayanan da muke da shi ya nuna cewa akwai kimanin almajirai miliyan biyiu a jihar mu da muke ganin babban barazana ce ga cigaban jihar mu.

"Duk da cewa gwamnati tana da ikon bullo da tsare-tsare domin magance matsalar almajiranci, amma a matakin kungiyoyi da daidaikun mutane akwai rawar da za mu iya takawa a kan wannan lamarin."

Akwai almajirai miliyan biyu a Zamfara - Gwamnatin Zamfara
Akwai almajirai miliyan biyu a Zamfara - Gwamnatin Zamfara
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sanusi: Ganduje ya yi martani ga Kwankwaso a kan zargin sa hannun Buhari

Ya yi kira ga iyaye da masu kulawa da yara su tabbatar sun sauke nauyin kulawa da yaransu domin rage kallubalen da ake fama da shi a cikin al'umma.

A jawabinsa, Direktan harkokin shari'a na majalisar jihar Zamfara, Mista Nasiru Jangebe ya dora laifi kan wasu malamai da ke yi wa ayoyin Kurani fasara ta kuskure domin halasta bara a cikin al'umma.

Jangebe ya ce barace-barace ba ta da alaka da neman ilimin Kur'ani.

Ya ce, "Malaman da ke wa'azi da kare bara da sunan musulunci ba su koyar da ainihin yadda addinin ya ke."

Jangebe ya yi kira ga gwamnatoci a dukkan mataki su bullo da shirye-shiryen da zau magance kallubalen bara a tituna da yara ke yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel