An yi rashin dalibi 1 yayinda gobara ta tashi a makarantar Albany

An yi rashin dalibi 1 yayinda gobara ta tashi a makarantar Albany

Shugabannin makarantar Albany International School, Zariya sun tabbatar da mutuwar dalibi daya dan ajin sakandare 3 mai suna Abdurahman Doko, a gobarar da ta tashi a dakin kwanan daliban makarantar ranar Laraba.

Gobarar wacce ta fara misalin karfe 2 na rana ta kona dakin kwanan dalibai maza dake unguwar Gaskiya Layout.

Diraktan makarantar, Dakta AbdulRaheem AbdulGaniyu, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai NAN cewa har yanzu ba a san abinda ya janyo gobarar ba.

Yace “A lokacin da gobarar ta fara, babu wuta a makarantar, kuma ba a yarda da girki a dakunan kwanan dalibai.“

“Dakin girkin abinci na da nisa da wajen kwanan. Saboda haka, bamu san yadda abin ya faru ba.“

Diraktan ya yabawa jamian kwana-kwana kan amsa kiran da sukayi na gaggawa da kuma takaita gobarar.

Abdulganiyyu ya kara da cewa daliban makarantar na hutu illa daliban karshe dake shirin jarabawar WAEC da UTME, da kuma masu shirin Juniro WAEC ke nan.

A cewarsa, a lokacin da gobarar ta far, dukkan daliban na azuzuwansu lokacin da gobarar ta kama.

An yi rashin dalibi 1 yayinda gobara ta tashi a makarantar Albany
An yi rashin dalibi 1 yayinda gobara ta tashi a makarantar Albany
Asali: Facebook

A bangare guda, Jamian hukumar yan sandan Najeriya sun samu nasarar ceto matasa masu bautar kasa hudu da masu garkuwa da mutane suka sace a ranar Litinin.

Kaakin hukumar yan sandan, DCP Frank Mba, ya bayyana hakan ne da daren nan a shafin sada zumuntar hukumar.

Yace "Dakarun hukumar yan sandan Najeriya a yai 11 ga maris 2020 sun ceto masu bautar kasa hudu da aka sace ranar 9 ga Maris a hanyar Funtua zuwa Gusau yayinda suka nufi sansanin yan bautar kasa dake Gusau, jihar Zamfara.

Yan bautar kasan sune Oladehin Paul, Ojo Temitope, Ojewale Elizabeth da Adenigbuyan Adegboyega kuma an mikasu da dirkatan hukumar NYSC na jihar Zamfara yayinda shi kuma Mohammed Ardo, wanda aka ceto tare da su an mikashi ha iyalansa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel