Mun kafa kwamitin binciken Ganduje - Hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano

Mun kafa kwamitin binciken Ganduje - Hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano

Hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano ta ce ta kafa kwamitin da zai binciki gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bisa zargin da ake yi masa na karbar cin hanci a cikin wasu faifan bidiyo da suka bulla a yanar gizo.

Shugaban kungiyar, Muhyi Magaji, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawarsa da jaridar Solacebase da ke garin Kano.

Ya fadi hakan ne yayin da yake martani a kan wani korafi da wata kungiya mai rajin samun shugabanni na gari a Kano (Kano Concerned for Prudent Leadership) ta shigar a gaban hukumar na neman ta binciki zargin da ake yi wa gwamnan.

Muhyi Rimin Gado ya ce hukumar ta mika korafin zuwa bangaren bincike domin gano gaskiyar zargin.

Mun kafa kwamitin binciken Ganduje - Hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano
Mun kafa kwamitin binciken Ganduje - Hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Shekau ya mayar da martani bayan saka kyautar $7m ga duk wanda ya kama shi (Bidiyo)

"Mun samu korafin bukatar mu binciki gwamna a kan zargin karbar cin hanci kamar yadda aka gani a wasu faifan bidiyo da suka bulla a yanar gizo. A maganar da nake yi yanzu, jami'anmu sun masu bincike sun fara aiki a kan zargin," a cewar shugaban hukumar.

Sai dai, Muhyi ya ce babu adireshi ko lambobin waya na wadanda suka aika korafin amma akwai sunan kungiya da sa hannnunsu.

"Mu na kira ga masu korafin da su kawo mana lambobin wayoyinsu domin tuntubarsu a duk lokacin da muke bukatar karin bayani daga wurinsu," a cewar Muhyi Rimin Gado.

A cikin korafin, kungiyar ta ce tana sane da cewa gwamna Ganduje yana da garkuwa yanzu, amma za a iya bincikensa tare da samunsa da laifi, idan yaso sai a jira ya sauka daga mulki sannan a gurfanar da shi a gaban kotu, kamar yadda hukumar EFCC ta yi wa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodole Fayose.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel