Yanzu-yanzu: El-Rufa'i ya kara baiwa Sanusi Lamido Sanusi wani mukamin ban girma

Yanzu-yanzu: El-Rufa'i ya kara baiwa Sanusi Lamido Sanusi wani mukamin ban girma

Gwamnatin jihar Kaduna ta alanta tunbukekken sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Cansalan jami'ar jihar Kaduna KASU.

Sanusi, zai maye gurbin Cansalan jami'ar na farko, Hakimin Moroa, Tagwai Sambo, wanda yake rike da mukamin tun shekarar 2005.

Sanarwa daga gidan gwamnatin jihar yace

“A madadin gwamnati da alummar jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, na farin cikin na Muhammadu Sanusi II a matsayin Cansalan jamiar jihar Kaduna.“

“A rayuwarsa ta gwamnati, ya nuna jajircewarsa wajen harkar Ilimi.“

“Babu shakka cewa cewa mai martaba, Sanusi II zai bayar da shugabanci na kwarai wajen daga mutuncin jamiar a Najeriya da kuma duniya.“

Wannan ya biyo bayan mukamin da gwamnatin jihar ta ba tubabben sarkin a jiya.

KU KARANTA Babu ruwan Buhari da lamarin saurautar Kano - Fadar shugaban kasa ta mayarwa Kwankwaso martani

Mun kawo muku cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta ba Muhammadu Sanusi II gurbin aiki bayan tube masa rawani da gwamnatin jihar Kano tayi a ranar Litinin.

Ta bashi gurbi ne a KADIPA, cibiyar habaka kasuwancin jihar.

A wata takarda da ta fito daga gidan Kashim Ibrahim, Gwamna Nasir El-Rufai ya amince da kafa shugabannin cibiyar KADIPA din.

An kafa cibiyar ne a 2015 kuma tana kan gaba ne wajen habaka kasuwancin jihar tare da saukakawa kasuwanci a jihar Kaduna. Bankin Duniya kuwa ya kalla cibiyar a matsayin ta farko a fannin kasuwanci a Najeriya.

Sanarwar da mai bawa gwamna shawara a fanin watsa labarai, Muyiwa Adekeye ya aike wa Premium Times a ranar Talata ta ce, “Malam Nasir El-Rufai ya amince da zaben mai martaba, Muhammadu Sanusi II matsayin mataimakin shugabancin KADIPA."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel