Idan mijina baya gamsar dani fita zanyi na nemi maza a titi - Juliet Njemanze
Fitacciyar jarumar fina-finan kudancin Najeriya Nollywood ta bayyana cewa matukar abokin rayuwarta baya gamsar da ita a bangaren jima'i to lallai babu yadda ta iya illa ta fita taci amanarshi
Jarumar ta bayyana hakane a wata hira da tayi da Vanguard.
A cewarta ko da za a bata duka kudin duniya, amma kuma bata gamsuwa a fannin jima'i to tabbas babu abinda zai hanata cin amanar abokin rayuwarta.
"A wajena banda bautar ubangiji babu abinda ya kai jima'i muhimmanci. Dole ya zama yana da kwazo a gado. Tabbas a wajena jima'i yafi kudi, saboda zaka bani duka kudin duniyar nan, amma idan baka gamsar dani dole zan fita na ci amanarka," cewar ta.
Sai dai kuma Njemanze ta ce ba za ta iya yin fim din batsa ba, saboda imanin da take da shi na addini, amma kuma za ta yi rungume-rungume sama-sama.
"Akwai abubuwan da ba zan iya yi ba a fim, idan har abinda za a sanya ni nayi a fim ya sabawa koyarwar addinina ba zan yadda nayi ba. Ba zan iya yin fim din batsa ba.
KU KARANTA: Rikici ya barke wajen rabon gado bayan matar mamacin ta gano cewa mijinta yayi auren sirri kafin ya mutu
"Zan iya fitowa nayi rungume-rungume a fim, amma ba zan iya zina a ciki ba. Ina matukar jin imani na a jikina. Ina son Allah, kuma ina karanta Bible ina addu'a."
Juliet Njemenze an haifeta a cikin garin Kano, tayi suna a harkar fim ne bayan ta fito a cikin fim din Obi Emenloye mai suna 'Calabash'.
Haka kuma ta fito a cikin fina-finai irin su 'Tears in my Heart', 'My Regret', 'Pharaoh Let My People Go', '15 Years of Slavery', 'My Friend My Pain', da kuma 'Avoidable Blunder'.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng