Sanusi II ya karbi mukaman da aka ba shi a Kaduna - El-Rufai

Sanusi II ya karbi mukaman da aka ba shi a Kaduna - El-Rufai

- Gwamna El-Rufai ya ce tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya karbi mukamai biyu da ya ba shi

- Gwamnan ya nada tubabben sarkin a matsayin shugaban gudanarwa na jami'ar Kaduna (KASU) da kuma mamba a kwamitin KADIPA

- El-Rufai ya mika godiyarsa ga tsohon sarkin saboda cigaba da bayar da goyon bayansa domin ganin jihar ta Kaduna ta cinma burinta

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce sarkin Kano Muhamamdu Sanusi II da aka sauke ya amince da nadin mukamen da ya yi masa a gwamnatin jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Jaridar ta ruwaito cewa Sanusi ya sanar da amincewa da karbar mukamin ne cikin wata sanarwa mai dauke da saka hannun hadimin Gwamna El-Rufai, Muyiwa Adekeye a ranar Laraba 11 ga watan Maris.

Sanusi II ya karbi mukaman da aka ba shi a Kaduna - El-Rufai
Sanusi II ya karbi mukaman da aka ba shi a Kaduna - El-Rufai
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Sarkin Loko ya bayyana abinda suka tattauna da Sanusi II a daren da ya kwana a garinsa

Gwamnan ya mika godiyarsa ga tsohon sarkin saboda cigaba da bayar da goyon bayansa domin ganin jihar ta Kaduna ta cinma burinta

A baya Legit.ng ta ruwaito muku cewa gwamnatin jihar Kaduna a ranar Laraba ta karrama tsohon sarkin da wani mukammi.

An nada tsohon sarkin a matsayin shugaban gudanarwa na jami'ar jihar Kaduna (KASU).

Sanusi zai maye gurbin Tagwai Sambo, Sarkin Moro'a, wanda shine shugaban gudanarwa na jam'iyyar tun da aka kafa ta a shekarar 2005.

An kuma nada Sanusi a matsayin mamba na hukumar inganta saka hannun jari na jihar ta Kaduna wato (KADIPA).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel