Bullar Coronavirus ya kawo cikas ga kudaden shigar Najeriya - Buhari

Bullar Coronavirus ya kawo cikas ga kudaden shigar Najeriya - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce bullar cutar Coronavirus ya shafi kudaden shiga da kasar ke samu

Sanarwar da kakakin shugaban kasar, Garba Shehu ya fitar ya ce Buhari ya yi wannan jawabin ne yayin da mambobin hadakar kungiyar ma'aikatan lafiya (JOHESU) suka kai masa ziyara a fadarsa a ranar Talata.

A yayin ziyarar, kungiyar ta bukaci shugaban kasar ya saka baki a cikin batun albashinsu da wasu batutuwa da suka shafi ma'aikatan lafiyar.

Coronavirus na shafar kudaden shiga da muke samu daga man fetur - Buhari

Coronavirus na shafar kudaden shiga da muke samu daga man fetur - Buhari
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kauyen Loko: Muhimman abubuwa 7 da ya kamata a sani game da masaukin Sanusi na farko

Da ya ke mayar da martani, shugaban kasar ya roki ma'aikatan lafiyar su ƙara haƙuri da gwamnatinsa duba da cewa kasar tana fuskantar wasu kalubale sakamakon bullar Coronavirus.

Ya basu tabbacin cewa gwamnatinsa na duba korafe-korafensu da niyyar warware musu matsalolin su kuma ya bukaci su cigaba da yin aiki domin cigaban kasar.

"Muna duba koken su amma ya kamata ku yi la'akari da halin da kasar ke ciki a yanzu. Coronavirus yana kawo mana tangarda," kamar yadda aka ruwaito shugaban kasar ya fadi.

"Yana shafar abinda muka fi dogara da shi wato man fetur hakan na nufin ya shafi kuɗin shiga da muke samu."

"Ku taimake mu yi wa mutanen ku bayani. Mu zama masu kishin kasa, mu lura da halin da gwamnati ke ciki kuma kame kai ... Ya zama dole su jadadda cewa akwai bukatar mu hada kan mu wuri guda domin inda muka bari son kai ya raba mu al'ammura za su tabarbare mana, saboda haka ku yi hakuri da mu."

Shugaban kasar ya kara da cewa gwamnatinsa ta yi nasara wurin tabbatar da cewa kasar ta fara dogaro da kanta wurin samar da abinda za a ci a cikin shekaru hudu da suka shude duk da karancin kudin shiga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel