Tirkashi: 'Yan sanda sun kama abokin aikinsu dan sanda a Adamawa

Tirkashi: 'Yan sanda sun kama abokin aikinsu dan sanda a Adamawa

Sabon rundunar tsaro ta hadin guiwa tsakanin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa da Fulani ‘yan sa kai a jihar ta fara samun nasara. Ta damke mutane 71 da ake zargi da garkuwa da mutane, fashi da makami da fyade. A ciki kuwa har da wani jami’in dan sanda.

A yayin amsa tambaya daga manema labarai, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Audu Madaki ya ce daga cikin wadanda ake zargin akwai wani dan sanda mai suna Abdulrazaq Dahiru mai mukamin sajan. A halin yanzu kuwa ana tuhumarsa ne tare da wasu mutane hudu da ake zargi da fyade, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Kamar yadda yace, “Wadanda ake zargin sun hada baki ne inda suka dinga sace mutane tare da garkuwa dasu a jihar. Sun karba kudin fansa ya kai naira miliyan uku da dubu dari takwas,."

“A ranar 8 ga watan Maris na 2020, a yayin da ake tuhumar masu garkuwa da mutanen, daya daga cikinsu ya bayyana cewa suna hada baki ne da wani Sajan Abdulrazak Dahiru,” yace.

Madaki ya kara da cewa, dan sandan da ake zargi yana samar musu da bindigogi ne da harsasai wanda ke taimaka musu wajen aiwatar da ta’addanci a jihar.

'Yan sanda sun kama abokin aikinsu dan sanda a Adamawa
'Yan sanda sun kama abokin aikinsu dan sanda a Adamawa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Buhari da gwamnan Nasarawa suna ganawa a Aso Rock

“A don haka ne rundunar ta damke dan sandan inda ake tuhumarsa,” ya kara da cewa.

Kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar ya sanar, an samu bindigogi kirar AK 47, harsasai 761, mujallu 18 da kuma kananan bindigogi 5.

A yayin jinjinawa ‘yan kungiyar sa kai ta Fulani daga kungiyar Miyetti Allah da Tabital-Puulaku, a kan yadda suka nuna jajircewarsu da taimakon jami’an tsaro.

Madaki ya ce 11 daga cikin masu garkuwa da mutanen sun mika kansu kuma sun yi alkawarin tsamo sauran ‘yan uwansu.

‘Yan sandan sun ce matasa 51 ne suka damke masu fashi da makami, wadanda suka addabi jama’ar jihar sun shiga hannu. An kama su ne a maboyarsu da ke Jambutu, Dobeli da Kofare dauke da miyagun makamai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel