Yanzu-yanzu: Buhari da gwamnan Nasarawa suna ganawa a Aso Rock
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Nasarawa, Mista Abdullahi Sule suna ganawa a halin yanzu.
Gwmana Sule ya iso fadar Aso Rock ne misalin karfe 10 na safe gabanin taron majalisar zartarwa na kasa da za a gudanar kamar yadda The Punch ta ruwaito.
A halin yanzu dai ba a san abinda gwamnan zai tattauna ba a ganawarsa da Shugaba Buhari.

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Kauyen Loko: Muhimman abubuwa 7 da ya kamata a sani game da masaukin Sanusi na farko
Jihar Nasarawa ce inda aka bawa tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II masauki a ranar Litinin bayan gwamnatin jihar Kano ta cire shi daga kujerar mulkin Kano.
Wata majiyar ta ce akwai yiwuwar gwamnan ya ziyarci shugaban kasar ne domin ya bashi bayani a kan halin tsaro da jihar ke ciki a halin yanzu.
A wani rahoton, mun kawo muku cewa gwamnatin jihar Kaduna ta ba Muhammadu Sanusi II gurbin aiki bayan tube masa rawani da gwamnatin jihar Kano tayi a ranar Litinin.
Ta bashi gurbi ne a KADIPA, cibiyar habaka kasuwancin jihar. A wata takarda da ta fito daga gidan Kashim Ibrahim, Gwamna Nasir El-Rufai ya amince da kafa shugabannin cibiyar KADIPA din.
An kafa cibiyar ne a 2015 kuma tana kan gaba ne wajen habaka kasuwancin jihar tare da saukakawa kasuwanci a jihar Kaduna.
Sanarwar da mai bawa gwamna shawara a fanin watsa labarai, Muyiwa Adekeye ya aike wa Premium Times a ranar Talata ta ce, “Malam Nasir El-Rufai ya amince da zaben mai martaba, Muhammadu Sanusi II zuwa shugabancin KADIPA."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng