Mutuwa ta yi awon gaba da hadiman gwamna guda 3 cikin kwanaki 5
Gwamnan jahar Delta, Ifeanyi Okowa ya shiga halin alhini da jimami biyo bayan mutuwar wasu hadimansa guda uku a jajjere cikin kwanaki biyar ta hanyoyi daban daban.
Jaridar Punch ta ruwaito daga cikin mamatan akwai babban hadimin gwamnan bai ikon zartarwa, Cif Amos Itihwe wanda ya mutu a baya baya, a ranar Talata, 10 ga watan Maris, bayan hadimai biyu da suka fara mutuwa.
KU KARANTA: Ministar kiwon lafiya ta kamu da cutar Coronavirus, ta killace kanta
Amos ya tama zama kwamishin kabila hukumar kula da yankunan dake da arzikin man fetir ta jahar Delta, haka nan ya taba zama shugaban jam’iyyar PDP a karamar hukumar Ughelli ta kudu, sa’annan ya rike mukamin hadimin gwamna a kan harkar siyasa.
A ranar Lahadin da ta gabata ma wani hadimin gwamnan mai suna Friday Akpoyibo ya mutu, yayin da hadimin da ya fara mutuwa, mai suna Cif Godspower Muemuifo ya mutu a ranar Laraba, 4 ga watan Maris bayan wata gajeruwar rashin lafiya.
Gwamna Okowa ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar abokan aikin nasa, kamar yadda ya sanar ta hannun mai magana da yawunsa, Olisa Ifeajika, inda ya jajanta ma iyalan mamatan tare da musu ta’aziyyar rashin da suka yi.
“A madadina da al’ummar jahar Delta ina mika ta’aziyyar mutuwar Cif Godspower Muemuifo, Friday Akpoyibo da Cif Amos Itihwe, mutuwarsu ya kadani sosai musamman kasancewarsu yan siyasa dake tare da al’ummarsu, sa’annan masu fada ma shuwagabanni gaskiya.” Inji shi.
A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jahar Kano, kuma wanda ya nada tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa tubuke rawanin Sarkin Kano umarni ne daga wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da ya yi game da batun tsige tsohon Sarkin na Kano, inda ya bayyana hakan a matsayin abin bakin ciki ga jahar Kano, Najeriya da ma duniya gaba daya.
A cewar Kwankwaso: "Shuwagabannin gwamnatin Kano da kansu ne su ke cewa umarni aka ba su, kuma shi ya ba su umarni….Shugaba Buhari yana tsoma hannu cikin al'amuran jihar Kano, Inda ya kamata ya sa hannun sai mu ga ba nan ya sa hannu ba, inda kuma bai kamata ya sa hannu ba, sai mu ga a nan ya sa hannu….sai dai musamman mu nan a Kano yadda muke gani yana hargitsa inda yake sa hannu".
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng