Ni ba budurwar El-Rufai bace - Hadiza Usman

Ni ba budurwar El-Rufai bace - Hadiza Usman

Shugabar hukumar tashar jiragen ruwa NPA, Hadiza Usman, ta karyata zargin da ake mata na cewar tana soyayya da gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kuma wai hakan ne yasa aka bata matsayin shugar NPA.

Hadiza Usman, wacce ta kasance shugabar ma’aikatan gwamnatin El-Rufai daga shekara ta 2015 zuwa 2016, ta bayyana hakane a wani hira da tayi da gidan talabijin na TVC ranar Litinin, ranar murnar zagayowar ranar mata ta duniya.

Tace zargin da ake mata na soyayya da El-Rufai, labarin kanzon kurege ne wanda ya dade yana yaduwa.

“Ni ba budurwasa bace, Gwamna El-Rufa’I shugabana ne kuma jagorana ne.”

“Ya taimaka mun matuka wurin cimma burina da burin ko wacce mace data yi aiki a karkashinsa”

“Kamar yadda kuka sani, Jihar Kaduna itace jiha ta farko da aka fara zaben mace ta zama mataimakiyar gwamna, toh anan zaku iya ganin cewa yana da son yasa mata a matsayi mai girma ta yadda za,a rage yada jita jita,” A cewarta

KU KARANTA Legas Sanusi ya zaba amma aka tilasta kaishi Nasarawa - Lauyan tsohon Sarkin

Ni ba budurwar El-Rufai bace - Hadiza Usman

Ni ba budurwar El-Rufai bace - Hadiza Usman
Source: UGC

Hadiza Usman mai kimanin shekaru 44, yar siyasa ce kuma yar fafutukan kungiyar kira da adawo da yan matan Chibok ce, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada ta a matsayin shugabar hukumar tashar jiragen ruwa a watan Yuli shekarata 2016.Nadin nata ya jawo cece cuce a wurin jama,a cewar bata dace da matsayin ba.

Shugabar, har ila yau, tace wannan yunkuri ne na karyawa mata gwiwa da suke da matsayi babba.

“Wannan shine abinda suke cewa mata dansu karya mana gwiwa, duk abinda kayi don nuna bajintarka akan aikinka, sai su jingina shi da cewa kana da alaka da wani ne,”

“Abin nufi anan shine, ka samu aiki kuma kana aiwatarwa yadda ya kamata, toh idan mutane suka fara cewa ka samu matsayin ne saboda kai budurwar wani ce, toh wannan shi ake kira da karya gwiwa,”.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel