Legas Sanusi ya zaba amma aka tilasta kaishi Nasarawa - Lauyan tsohon Sarkin

Legas Sanusi ya zaba amma aka tilasta kaishi Nasarawa - Lauyan tsohon Sarkin

Abubakar Mahmoud, babban lauyan Sanusi Lamido Sanusi, tsohon sarkin Kano, ya ce bayan sauke sarkin daga mulki, ya zabi a mayar da shi jihar Legas amma aka tilasta masa zuwa Nasarawa.

A hira da manema labarai ranar Talata, Mahmoud ya ce yana wajen lokacin da aka kawo wa sarkin takardar kwance masa rawani.

Ya ce kwamishanan yan sandan jihar ya hana Sanusi zuwa jihar zabinsa inda yace umurin da aka bashi a cikin wasika shine a kaishi Nasarawa - kuma sai ya bi umurnin.

Legas Sanusi ya zaba amma aka tilasta kaishi Nasarawa - Lauyan tsohon Sarkin

Lauyan tsohon Sarkin
Source: Facebook

KU KARANTA Hotunan sabon sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, da baka taba gani ba

A cewar “Mun sanar da kwamishanan yan sandan cewa kaishi Nasarawa sabanin zabinsa take hakkinsa na dan Adam ne kuma ya sabawa doka.“

“Sarkin ya sanar da kwamishanan cewa abokansa sun turo masa jirgin da zata daukeshi da iyalansa zuwa Legas, kawai abinda suke bukata shine jamian tsaron da zasu tabbatar musu da tsaro a hanya.“

“Kwamishanan ya ki, yace ba umurnin da aka bashi kenan ba. Sun amince a kai iyalansa Legas amma shi aka garzaya da shi Abuja kafin zuwa da shi jihar Nasarawa.“

“Gudun kada ya sanya rayuwarsa ko na iyalansa cikin hadari, Sarkin ya amince kuma ya tafi da jamian tsaron.“

Lauyan ya ce daga Abuja, sai da Sanusi ya kwashe awanni bakwai ana tafiya zuwa wata kauyen jihar Nasarawa.

Mahmoud ya ce an yi hakan ne domin gajiyar da sarkin kuma kowa ya gaza samun sa a waya ranar.

Ya yi kira ga yan Najeriya da kasashen waje da kuma masu ruwa da tsaki su sanya baki cikin lamarin domin kare rayuwar tsohon sarkin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel