Aikin rusau: An baiwa hammata iska tsakanin yan kasuwa da jami’an gwamnati a Abuja
Hankula sun tashi a kasuwar zamani ta Dutse dake babban birnin tarayya Abuja sakamakon rikici daya kaure tsakanin yan kasuwa masu shaguna da kuma jami’an hukumar dabbaka doka ta babban birnin tarayya Abuja a kokarinsu na rushe shagunan.
Sahara Reporters ta ruwaito wannan rikici ya yi kamari inda ta kai ga har yan kasuwar suka banka ma ofishin hukumar wuta dake cikin kasuwar, sa’annan suka tare babbar titin da ta ratsa ta gefen kasuwar.
KU KARANTA: Ba’a nan take ba: Sanusi zai iya komawa kujerarsa – inji babban lauyansa

Asali: Facebook
A ranar Lahadin da ta gabata ne jami’an hukumar suka jibge manyan motocin aikin rusau irinsu katapila da sauransu a kasuwar Dutse, inda daga bisani suka rushe duk wasu shagunan wucin gadi da ba’a samar dasu a kan ka’ida ba.
Sai dai wani dan kasuwar ya bayyana ma majiyar Legit.ng cewa hukumar babbar birnin tarayya Abuja ta baiwa yan kasuwa wuri domin su bude shagunan wucin gadi saboda basu da karfin kama hayan shago a kasuwar.

Asali: Facebook
Kwatsam kuma sai hukumar ta basu wa’adin tashi na yan kwanaki kadan, inda ta bayyana musu cewa ta sayar da wuraren da suka gina shagunan nasu na wucin gadi, wannan ne ya fusata yan kasuwar, suka diran ma jami’an hukumar tare da lalata musu kayan aiki.
Daga bisani jami’an Yansanda sun isa kasuwar, inda suka tarwatsa jama’a da barkonon tsohuwa.

Asali: Facebook
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng