Babu gwamnatin da zata zura ido ana sukarta kamar yadda Sunusi yake yi – Hadimin Ganduje

Babu gwamnatin da zata zura ido ana sukarta kamar yadda Sunusi yake yi – Hadimin Ganduje

Daga cikin laifukan da suka sa gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tsige Muhammadu Sunusi II a matsayin Sarkin Kano akwai yawan sukar gwamnatin jahar da yake yi, inji hadimin gwamnan, Salihu Tanko Yakasai.

Yakasai ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels a ranar Talata, inda yace babu wani mai mulki da zai lamunci irin caccakar da Sunusi ya yi ma Gwamna Ganduje a bainar jama’a.

KU KARANTA: Ba’a nan take ba: Sanusi zai iya komawa kujerarsa – inji babban lauyansa

A cewarsa Yakasai, Sunusi na da daman ganin Sarki a duk lokacin da ya so, don haka kamata ya yi ace yan tattaunawa da gwamnan idan sun hadu daga shi sai shi, ba wai a bainar jama’a ba.

“Sarkin nada daman ganin gwamna a duk lokacin da ya so, da ya yi amfani da wannan damanmaki wajen baiwa gwamnan shawara, amma sai ya gwammace ya yi amfani da munbari da tarukan jama’a wajen baiwa gwamnati shawara, wanda hakan bai dace ba.

“Don haka zaka iya fahimtar sallamar tasa a matsayin siyasa da ko ma menene, amma maganan gaskiya shi ne babu wanda zai kyale irin wannan cin mutunci bayan kana da daman ganinsa. Misalin sukar da ya yi ma gwamnati a lokacin da ta yi yunkurin gina layin dogo a cikin gari.” Inji shi.

“Tun da aka raba masarautun Kano, an gudanar da taruka daban daban da gwamnatin jahar ta shirya wanda aka gayyaci Sarkin amma ya ki zuwa, ina tabbatar maka da cewa Sarkin bai halarci taron kaddamar da ilimi kyauta da gwamnatin jahar ta shirya ba

“Wanda ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, kowa na da daman fadin albarkacin bakinsa, amma wadannan ne dalilan da suka gwamnan ya cire Sarkin.” Inji shi.

Da aka tambayeshi ko wadannan dalilai sun isa su sa a tsige Sarki, sai Yakasai ya tabbatar da hakan, inda yace tabbas sun isa saboda sun saba ma kundin dokokin masarautar Kano.

Daga karshe Yakasai ya bayyana cewa hatta tsohon gwamnan jahar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso sai da ya baiwa Sarki Sunusi takardar gargadi sau hudu a iya zaman da suka yi, don haka yace kamata yayi a yaba ma Ganduje da ya dade yana hakuri da shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel