PDP ta yi martani a kan sauke Sanusi II daga karagar mulki

PDP ta yi martani a kan sauke Sanusi II daga karagar mulki

Jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana damuwarta bayan sauke sarkin Kano, Muhammadu Sanusi daga kujerarsa da gwamnatin jihar Kano ta yi kamar yadda The Punch ta ruwaito.

A ranar Litinin ne gwamnatin jihar ta Kano ta sanar da cire Sanusi a matsayin sarkin Kano.

Sakataren gwamnatin jihar, Usman Alhaji ne ya bayar da sanarwar a yayin taron masu zartarwa a jihar.

Ya ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya cire sarkin ne saboda zarginsa da rashin biyaya ga umurni da gwamnatin jihar ke bawa masarautar.

DUBA WANNAN: Na sadu da kanwa ta har sau 3, babu wani aibu a saduwa da 'yan uwan ka - Wani dan Najeriya

A sanarnar da ta fitar a shafinta na Twitter a ranar Litinin, jam'iyar ta ce an cire sarkin ne a lokacin da bai dace ba amma ta yi kira ga al'ummar jihar su kasance cikin lumana da bin doka.

Wani sashi na sanarwar ya ce: "Cire sarkin Kano: PDP ta bayyana damuwar ta, ta yi kira ga al'umma su kwantar da hankulan su."

A wani rahoton kun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ta ba Muhammadu Sanusi II gurbin aiki bayan tube masa rawani da gwamnatin jihar Kano tayi a ranar Litinin.

Ta bashi gurbi ne a KADIPA, cibiyar habaka kasuwancin jihar. A wata takarda da ta fito daga gidan Kashim Ibrahim, Gwamna Nasir El-Rufai ya amince da kafa shugabannin cibiyar KADIPA din.

An kafa cibiyar ne a 2015 kuma tana kan gaba ne wajen habaka kasuwancin jihar tare da saukakawa kasuwanci a jihar Kaduna. Bankin Duniya kuwa ya kalla cibiyar a matsayin ta farko a fannin kasuwanci a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel