Wani jika ya jibga kakar shi saboda fasto ya ce mayya ce (Bidiyo)

Wani jika ya jibga kakar shi saboda fasto ya ce mayya ce (Bidiyo)

- Wani ma’aboci amfani da kafar sada zumunta twitter mai suna samitauma ya wallafa wani bidiyo mai cike da tausayi da alhini

- Bidiyon na dauke da wani mutum da ke zane kakar shi bayan fasto ya ce mishi mayya ce

- Mawallafin bidiyon yayi Alla-wadai da wannan jika tare da faston da ya tsaya tsayin daka wajen ganin ya tarwatsasu

Wani ma’aboci amfani da kafar sada zumunta twitter mai suna samitauma ya wallafa wani bidiyo mai cike da tausayi da alhini. Bidiyon na dauke da wani mutum ne da ke zane kakar shi bayan fasto ya ce mishi mayya ce.

Kamar yadda jaridar Information,ng ta ruwaito, ya fada tsohuwar da duka ne ba ji, ba gani da baukatar ta amsa laifinta.

A yayin wallafa bidiyon, ya rubuta: “Kalla yadda wani mutum ke jibgar kakarshi bayan mugun fasto ya ce mayya ce. Ina fatan bai kashe wannan tsohuwar matar ba. Wasu fastocin suna da matsala kuma sun dage sai sun tarwatsa iyalai.”

KU KARANTA: Kwararon robar wadanda suka kwanta damu muke kaiwa bokaye - Karuwai

Ba wannan bane karo na farko da fastoci ke ire-iren hakan ga al'umma. Sannanen abu ne idan aka ce fastocin Najerya da na nahiyar Afrika sun saba cin karensu babu babbaka.

A kwanakin baya, Legit.ng ta ruwaito yadda wani fasto ya hada wani tafki a cikin farfajiyar cocinshi wacce ya kira da tafkin waraka. Faston nan na bari a shiga tafkin ne bayan an biya shi dubu hamsin.

Ga marasa halin biyan dubu hamsin kuwa, suna biyan dubu goma don a dibar musu ruwan a gora.

Faston ya sanar da mabiyan shi cewa ruwan tafkin na maganin ciwuka kuma yana yaye damuwa da talauci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel