Yadda wani matashi ya tarwatsa kwakwalwar budurwarsa mai juna biyu

Yadda wani matashi ya tarwatsa kwakwalwar budurwarsa mai juna biyu

- Rundunar ‘yan sandan jihar Katisna ta damke wani matashi mai shekaru 27 a kan laifin kisan kai

- Kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan ya sanar, an zargi matashin ne da kashe budurwar shi mai shekaru 14 a duniya

- Ya yaudareta ne zuwa wani daji inda ya shaketa tare da buga kanta da dutse sakamakon rikicin da suke na mai cikin da ke jikinta

Wani matashi mai shekaru 27 mai suna Shafi’u Haruna ya shiga hannun rundunar ‘yan sandan jihar Katsina bayan da aka zargesa da kashe wata karamar yarinya mai suna Hamsiya Lawal.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, wanda ake zargin ya kashe yarinyar ne sakamakon rashin jituwar da suka samu a kan mamallakin cikin da ke jikinta.

A wata takarda da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah ya fitar, ya ce Haruna yayi ikirarin cewa yarinyar budurwarshi ce.

Yadda wani matashi ya tarwatsa kwakwalwar budurwarsa mai juna biyu
Yadda wani matashi ya tarwatsa kwakwalwar budurwarsa mai juna biyu
Asali: UGC

KU KARANTA: Kwararon robar wadanda suka kwanta damu muke kaiwa bokaye - Karuwai

Wanda ake zargin ya kasheta ne a watan Disamban 2019 a kan fadan da suka yi na wanda ke da cikin jikinta.

Bayan aikata laifin kisan kan, Haruna ya boye amma an kama shi ne a ranar Talatar da ta gabata.

Kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan ya sanar, Haruna ya yaudari yarinyar ne zuwa wani daji da ke kusa da kauyensu inda ya shaketa tare da buga mata dutse a kanta. A take kuwa kwakwalwarta ta tarwatse wanda hakan yayi sanadin mutuwarta a take.

Nan ba dadewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel