Sanusi II ya dade da sanin cewa za a sauke shi daga karagar mulki - Majiya daga fada

Sanusi II ya dade da sanin cewa za a sauke shi daga karagar mulki - Majiya daga fada

Daily Trust ta ruwaito cewa a daren ranar Lahadi an tura jami'an tsaro inda suka mamaye fadar sarkin Kano bayan an tsige Muhammadu Sanusi II daga kujerar sarautar jihar.

Wata majiya ta bayyana cewa tsohon sarkin ya dade da sanin cewa za a tsige shi.

Majiyar ta ce: "Muna zaune a harabar fadar muka lura cewa an fara kwashe wasu kayyakin sarkin da muka tambayi dalili dai aka ce mana akwai yiwuwar za a cire sarkin.

"Amma babu wani abu da mutum zai iya yi domin canja lamarin... Tun a jiya mai martaba ya fara kwashe wasu kayayyakinsa daga fadar saboda ya san cewa za a cire shi."

Wata majiyar kuma ta ce, Sanusi da ke zaune da 'ya'yansa da matansa a fadar ya kashe makuden kudi domin yi wa fadar gyara. "Ya kashe makuden kudi domin gyara fadar ta dace da matsayinsa. Ya yi imanin cewa zai rayu a fadar har lokacin mutuwarsa."

Sanusi ya dade da sanin cewa za a tube masa rawaninsa

Sanusi ya dade da sanin cewa za a tube masa rawaninsa
Source: UGC

DUBA WANNAN: Na sadu da kanwa ta har sau 3, babu wani aibu a saduwa da 'yan uwan ka - Wani dan Najeriya

A jiya ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin sabon sarkin Kano awanni kadan bayan cire Sanusi II a matsayin sarki.

An tura tubabben sarkin zuwa jihar Nasarawa a garin Loko ya zauna a halin yanzu.

Awanni kadan bayan tsige shi, Sanusi ya sauka a filin tashi da saukan jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja daga nan kuma aka dauke shi a mota zuwa Loko a jihar Nasarawa.

Wata kwakwarar majiya ta ce tsohon sarkin bai nuna alamar damuwa ba a fili duk da halin da ya tsinci kan sa a ciki.

Majiyar ta ce, "Yana cikin natsuwa sosai," Majiyar ta kara da cewa, "Na yi magana da shi, Bisa ga dukkan alamu lafiyarsa kalau, ya ce min lafiyarsa kalau; Ya ce ba bai wa Allah mahallici komai a hannunsa."

Lauyan Sanusi, A.B. Mahmud SAN ya bayyana cewa cire Sanusi ya saba wa doka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel