Da Tambuwal bai zarce ba shima Sarkin Musulmi da an tsige shi - Shehu Sani

Da Tambuwal bai zarce ba shima Sarkin Musulmi da an tsige shi - Shehu Sani

Tsohon dan majalisar tarayyya mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya ce idan ba don Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya lashe zabensa na zarcewa karo na biyu a kan mulki ba da an tsige Sarkin Musulmi kuma shugaban kwamitin kolin musulunci na kasa, Muhammad Sa'ad Abubakar II.

Shehu Sani ya yi wannan lafazin ne a lokacin da ya ke tsokaci a kan tsige tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a ranar Litinin.

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje nan take ya amince da nadin Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano.

DUBA WANNAN: Na sadu da kanwa ta har sau 3, babu wani aibu a saduwa da 'yan uwan ka - Wani dan Najeriya

A cewar Shehu Sani a rubutun da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta na Twitter, Idan ba domin Tambuwal ya yi nasarar sake cin zabe a matsayin gwamnan jihar Sokoto ba a babban zaben 2019 shima 'shima sarkin musulmi da ke bayyana ra'ayoyinsa a kan abubuwan a ke faruwa a kasar da an tsige shi.'

A wani rahoton muk kawo muku cewa tsohon sanatan Najeriya wanda ya wakilci jihar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai karo ta takwas, Shehu Sani, ya kuma kalubalanci gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano a kan tube rawanin Sarkin Kano na 14 Malam Muhammadu Sanusi II.

An tube rawanin Sanusi ne a ranar Litinin, bayan an zargesa da rashin da’a ga ofishin gwamnan jihar da sauran cibiyoyin gwamnatin jihar, kamar yadda sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji ya sanar.

A yayin martani a shafinsa na twitter, tsohon sanatan ya ce wadanda suka tube rawanin Sarki Sanusi din sun yi hakan ne sakamakon giyar mulki da ke dibarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel