Waiwaye: Muhimman bayanai kafin hawan Sanusi mulkin Kano

Waiwaye: Muhimman bayanai kafin hawan Sanusi mulkin Kano

Bayan shekaru 5,watanni shida da kwana 26 da hawa mulkinsa, gwamnatin Kano a karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Ganduje ta kwance rawanin sarki na 14 a kano, Malam Muhammadu Sanusi II akan rashin girmama gwamnatin Jihar Kano da wasu hukumomin gwamnatin.

Ga wasu abubuwan da suka faru kafin hawan Sanusi Lamido kujerar Dabo:

Sarkin Kano na 13, Alhaji Ado Abdullahi Bayero ya rasu ranar juma’a, 6 ga watan Yuni 2014, bayan gajeruwar rashin Lafiya.

An gabatar da sunayen Sanusi Lamido, Alhaji Sanusi Ado Bayero da Wamban Kano, Alhaji Abbas Sanusi matsayin wadanda ke zawarcin kujerar marigayin.

Bayan kwana biyu da rasuwarsa ne aka nada Muhammadu Sanusi II da amincewar Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso.

Kafin nadinsa, Sanusi ya kasance masanin tattalin kuma ma'aikacin banki ne.

Yayi aiki a matsayin gwamnan babban bankin Nigeria daga shekara ta 2019 zuwa 2014, kafin Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dakatad dashi bayan ya yi zargin cewa $20bn sun bace a asusun gwamnati.

Kakansa Muhammadu Sanusi I yayi mulki daga 1953 zuwa 1963, kafin Ahmadu Bello ya sauke shi.

Mahaifinsa, Aminu Sanusi bai hawa mulkin Dabo ba, ya rasu yana matasayin ciroman Kano.

Marigayi Sarki Ado Bayero ya nada Sanusi Dan Majen Kano a shekara ta 2012.

Tsohon gwamnan babban bankin Nigeria ya zama shine sarki na 14 a jihadin da Usman Dan Fodio yayi na kafuwar daular Fulani.

Waiwaye: Muhimman bayanai kafin hawa mulkin Sanusi a Matsayin Sarkin Kano

Sarkin Kano
Source: UGC

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel