Shehu Sani ya yi 'jirwaye' a kan tube rawanin Sarki Sanusi II

Shehu Sani ya yi 'jirwaye' a kan tube rawanin Sarki Sanusi II

Tsohon sanatan Najeriya wanda ya wakilci jihar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai karo ta takwas, Shehu Sani, ya kalubalanci gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano a kan tube rawanin Sarkin Kano na 14 Malam Muhammadu Sanusi II.

An tube rawanin Sanusi ne a ranar Litinin, bayan an zargesa da rashin da’a ga ofishin gwamnan jihar da sauran cibiyoyin gwamnatin jihar, kamar yadda sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji ya sanar.

A yayin martani a shafinsa na twitter, tsohon sanatan ya ce wadanda suka tube rawanin Sarki Sanusi din sun yi hakan ne sakamakon giyar mulki da ke dibarsu.

Shehu Sani ya yi 'jirwaye' a kan tube rawanin Sarki Sanusi II
Shehu Sani ya yi 'jirwaye' a kan tube rawanin Sarki Sanusi II
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Babu bata lokaci: Tubabben Sarkin Kano ya kammala shirin barin fada, zai bar Kano

Tube rawanin Sanusi na wakiltar rashin zaman sarauta da gaskiya waje daya da rashin son kokarin gyaran al’adu masu bukatar gyara a Arewa. Ya kara da bayyana rashin juriya ta gwamnati da kuma giyar mulki,” ya wallafa.

Kamar yadda ya kara da cewa, “Dattawan da aka tura na arewa don kwantar da tarzomar da ke tsakanin gwamnan da sarkin sun kasa yin hakan amma kuma sai suka janye ba tare da sun sanar ba, inda suka bar wutar na ruruwa.

“Idan da Gwamnan Tambuwal bai samu zarcewa ba a jihar Sokoto, toh ba shakka hakan ce za ta faru tsakanin wanda aka zaba da sarkin Musulmai.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel