Musulmai sun gudanar da taron rokon Allah a jahar Katsina a kan matsalar tsaro

Musulmai sun gudanar da taron rokon Allah a jahar Katsina a kan matsalar tsaro

An gudanar da addu’o’i na musamman domin neman Allah madaukakin Sarki ya kawo agaji bisa matsalolin tsaro da suka addabi yankunan jahar Katsina, da ma kasa Najeriya gaba daya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito babban limamin masarautar Katsina, Malam Mustapha Gambo ne ya jagoranci daruruwan al’ummar Musulmai daga bangarori daban daban wajen gudanar da sallolin da addu’o’in.

KU KARANTA: Harin ta’addanci a Masallaci ya jikkata Musulmi 1 a kasar Faransa

Musulmai sun gudanar da addu’ar rokon Allah a jahar Katsina a kan matsalar tsaro
Musulmai sun gudanar da addu’ar rokon Allah a jahar Katsina a kan matsalar tsaro
Asali: Facebook

Babban limami Malam Mustapha ya bayyana bukatar dake da akwai na Musulmai su yi karatun ta natsu game da halayensu, sa’annan su nemi gafarar Allah domin ganin karshen wannan musifa da ake fama da ita.

Malam ya kara da nanata cewar Musulmai su dage su cigaba da neman taimakon Allah a duk lokacin da matsaloli suka fitine su, domin kuwa babu wani abu da ya fi karfin Allah Ya sauya shi.

Shima a jawabinsa, Sheikh Ismail Alkashnawi ya bayyana cewa malamai da dama sun daina gudanar da wa’azuzzuka kamar yadda ya kamata saboda wasu dalilansu na kashin kai, ya cigaba da cewa an daina zuwa kauyuka wa’azi sai dai a birane kadai.

Sheikh Kashnawi ya danganta matsalar yan bindiga ga jahilci, saboda a cewarsa mutum mai ilimi ba zai shiga harkar sata da kashe kashe ba.

Shi mai gayya mai aiki, wanda ya shurya gangamin, hadimin gwamna jahar Katsina a kan wayar da jama’a, Abdulaziz Maituraka ya bayyana cewa addu’o’i na warware duk wasu matsalolin da suka shafi jama’a, don haka yana da yakinin za su magance wadannan matsaloli dake damun Katsina da Najeriya.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Katsina ta samu nasarar damke wuyar wani gawurtaccen barawon mutane da ya shahara wajen sata tare da garkuwa da mutane a jahar Katsina da kewaye.

Kakakin Yansandan jahar, SP Gambo Isah ne ya bayyana haka a ranar Lahadi yayin da yake ganawa da manema labaru, inda yace Yansanda sun kama mutumin ne a ranar 7 ga watan Maris.

SP Gambo ya bayyana sunansa kasurgumin barawon a matsayin Kabiru Lawal dan shekara 30 mazaunin Ruwan Godiya a jahar Katsina, inda yace sun kama shi ne da misalin karfe 11:30 na dare.

Kaakakin yace asirin Kabiru ya tonu ne a daidai lokacin da shi tare da sauran miyagun abokansa suka kai farmaki gidan wani mutumi Alhaji Nasiru Ibrahim dake Rugar Kadi, a kauyen Ruwar Godiya a karamar hukumar Faskari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel