Da yiwuwan Najeriya ta sake shiga matsin tattalin arziki yayinda farashin mai ya fadi warwas

Da yiwuwan Najeriya ta sake shiga matsin tattalin arziki yayinda farashin mai ya fadi warwas

- Sabani tsakanin Saudiyya da Rasha ya janyo faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya

- A ranar Litinin, 9 ga Maris, farashin ya fado $31 ga ganganar mai daga kimanin $50

Bayan alaka ta shekara da shekaru tsakanin kasar Rasha da Saudiyya kan farashin man fetur a kasuwar duniya, an samu sabani kuma hakan ya shafi dukkan sauran kasashe masu arzikin man fetur.

Tun shekarar 2016, kasashen biyu sun hada kai wajen jagorancin kasashe masu arzikin man fetur a duniya.

A cewar rahoton The Economist, mambobin kungiyar kasashe masu fitar da man fetur wato OPEC, sun yi kokarin yin yarjejeniya kan adadin danyen man da za'a rika fitarwa.

Amma a ranar Juma'a, 6 da Maris, maimakon yarjejeniyar da aka bukaci yi, an yi baran-baran a ganawar saboda kasar Rasha ta ki amincewa da rage adadin man feturin da zata rika fitarwa kuma hakan bai yiwa Saudiyya dadi ba.

Ba tare da bata lokaci ba kasar Saudiyya ta karya farashin man feturin da kimanin kashi 30%.

A ranar Juma'a da aka kammala ganawar, farashin gangar man fetur a kasuwar duniya ta fado daga $50 zuwa $45, amma a ranar Litinin, ta fado warwas zuwa $31.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel